Connect with us

LABARAI

An Shawarci Al’ummar Hausawa Kan Su Rungumi Jaridun Hausa

Published

on


Daga Balarabe Abdullahi, Zariya

Wani mai kishin harshen Hausa, kuma dan kasuwa a Zariya, mai suna Alhaji Hashimu Mai kashu, ya bayyana matukar damuwarsa da yadda mafiya yawan al’ummar Hausawa ba su damu da sayen jaridun da ake buga su da harshen Hausa ba, sai dai jaridun Ingilishi suka fi mayar da hankalinsu a kai, Alhaji Hashimu mai kashu ya bayyana hakan ne jim kadan bayan wata jarida mai suna TASKIRA ta karrama shi a Zariya, kan ayyukan tallafa wa al’umma da yake yi a sassan Zariya da kewaye.

A cewar Mai kashu, yadda jaridun Hausa ke fito wa  irin fitowar murucin kan dutse, amma, in ji shi,sai a wayi gari ba su, ba alamunsu, a dalilin sakaci da rashin kishin Hausawa musamman manyan ‘yanboko da kuma masu hannu da shuni.

Alhaji Hashimu,wanda kuma shi ne tsohon shugaban ‘yan kasuwar Dan-magaji a Zariya, ya ce lokaci ya yi da ‘yankasuwa da manyan ‘yanboko za su rika bayar da tallace-tallacensu a jaridun Hausa, domin masu buga jaridun su samu saukin fuskantar matsalolin da suke fuskantar matsalar rashin kudi, a duk lokacin da suka tashi buga jaridun na su.

Da ya juya ga ma su jagorantar al’umma, tun daga kananan hukumomi zuwa jihohin da suke Arewacin Nijeriya, sai ya shawarce su da su rika amfani da jaridun Hausa wajen sanar da jama’arsu abubuwan da suke yi musu, da kuma abubuwan da suke bukata al’ummomin da suke mulkarsu su yi musu.

Ga jaridun kuwa ya nuna matukar gamsuwarsa da yadda wasu ke mayar da hankalinsu ga labaran da suka shafi masu karanta jaridun. Ya ce wannan na daga cikin dalilan da suka sa a duk lokacin da jaridun suka fito, masu sayen jaridun ke daukar jaridun tamkar mahadin Karin-karin kumallo a garesu.


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI