Connect with us

LABARAI

Rundunar ‘Yansanda Ta Kira Taron Tattaunawa Tsakanin Makiyaya Da Manoma

Published

on

A yunkurinta na tabbatarda zaman lafiya a birane da yankunan karkarar jihar Jigawa rundunar ‘yansanda reshen jihar ta gabatar da wani taron tattaunawa da juna tsakanin fulani da manoma.

Taron wadda aka gabatar a karamar hukumar Kiri-kasamma ya sami jagorancin Kwamishinan ‘yansanda na jihar CP Bala Zama Senchi da sarkin Hadeja Alhaji Maje Abubakar Haruna.

Kwamishinan ‘yansandan ya bayyana cewa, sun shirya wannan taro ne tsakanin makiyaya da Manoman yankin masarautar Hadejia wadda ya hadarda kananan hukumomi takwas dake karkashin masarautar.

Haka kuma ya ce muhimmin tara manoman da makiyayan shine don a zauna a tattauna tareda baje kolin matsaloli dake haifar da sabani tsakani gamida bada shawarwari tareda zana jadawalin da zai kawo karshen rikici a yankin baki daya.

Kwamishinan ya kuma nemi goyon bayan al’ummar yankin da su tallafawa hukumar ‘yansandan ta hanyar fallasa duk wani da ake zargi da karya doka ko kuma ake zargin mai laifi ne domin daukar matakin da ya dace akansa.

Shima da yake nasa jawabin a yayin tattaunawar, Mai martaba sarkin Hadeja Alhaji Abubkar Maje Haruna, ya bayyana cewa al’umma su kara kaimi wajen fallasa masu aikata laifuka domin daukar matakan da suka dace akansu.

 

 
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: