Mun Kamo Wadanda Suka Kai Wa Mawaka Hari A Bauchi, In ji ‘Yan Sanda — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Mun Kamo Wadanda Suka Kai Wa Mawaka Hari A Bauchi, In ji ‘Yan Sanda

Published

on


Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta bayyana cewar ta samu nasarar kamo ‘yan sara suka guda tara 9 wadanda suka kai wa mawaka hari a lokacin da suke tattauna yadda za su yi su inganta aiyukansu a wata dakin tantane murya ta Shamaki Media da ke cikin Insurance House a Bauchi inda suka jikkata wasu daga cikin mawakan.

Kakakin Rundunar ta jihar Bauchi, DSP Kamal Datti Abubakar shi ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwar da ya aiko wa manema labaru a jiya, ya ke cewa tun bayan aukuwar lamarin ne suka baza komarsu domin ganowa gami da kamo ‘yan sara sukan da suka yi wannan mummunar ta’asar.

Ya ce “Bayan faruwar lamarin, an kai wa ofishinmu da ke GRA rahoton aukuwar hakan a ranar 18/4/2018 inda aka ce da misalin karfe 1330hrs wasu ‘yan sara suka dauke da muggan makamai da suka kunshi adduna da sauran makamai masu illa sun farmaki wani ofishi da ke cikin Re-Insurance House da ke kan titin Ahmadu Bello Way, Bauchi.

“A sakamakon wannan harin, wasu da dama sun gamu da munanan raunuka, wasu ma sun karye,”

Ya ci gaba da cewa, “Daga cikin wadanda suka samu raunuka a harin sun hada da Aliyu Shamaki, Haruna Aliyu, Nazir M. Nazir, da Danjuma Hassan sai kuma Jibrin wanda aka fi sani da JB,”

Ya bayyana cewar wadannan mutane biyar dukkaninsu sun gamu da munanan raunuka a sakamakon farmakin.

 

DSP Kamal Datti Abubakar ya bayyana cewar bayan da suka samu labarin aukuwar lamarin ne kuma gamayyar sashinsu na ofishin GRA da hadin guiwar sashin musamman masu dakile aikace-aikacen ‘yan fashi da makami wato (FSARS) suka dauki kwakwaran matakin ganowa gami da kamo wadanda suka kai wannan harin domin gurfanar da su a gaban kuliya, cikin ikon Allah kuma sun samu nasarar hakan.

Ya ce, mutane tara ne suka samu nasarar kamawa wadanda kuma suke zarginsu da hanu dumu-dumu kan kai wannan farmakin, ya jeru sunayensu kamar haka: Alhaji Sunusi mai shekaru 35 wanda kuma shine jagoan kai harin, sai kuma Musa Mohnammed 25,  Ashiru Suleiman 25,  Abubakar Bello 20,  Usman Abubakar 20,  Jamilu Garba 21.

Sauran su ne Yusuf Dahiru 25 wanda aka fi sani da Eminem, Abdulazeez Dabo

da kuma Kabiru Inuwa 22.

Kadan daga cikin kayayyakin da ‘yan sandan suka kwamo a hanun ‘yan sara sukan sun hada da adduna guda hudu, sharbebiyar wuka mai tsayin gaske uda daya, da kuma wasu tabar wiwi da ake zargi.

DSP ya bayyana cewar dukkanin wadnada suka kaman sun amsa da bakunansu kan cewar sun kasance kan wajen kai wannan harin, a don haka ne ma tun a jiran rundunar ta gurfanar das u a gaban kotu domin su fara fuskantar shari’a daidai da laifinsu “Sun amsa da bakunsu kan cewar sun aikata laifin na, don haka a yau (jiya kenan) 20/04/2018 mun gurfanar da su a gaban kotu,”.

Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta kuma shawarci dukkanin jama’an jihar da cewar suke kai rahoton aukuwar dukkanin wani sara suka ko kuma kai labarin dukkanin wani dan sara suka zuwa ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa ko kuma jama’an jihar su tuntubi rundunar ‘yan sandan akan layinsu ta kar-ta-kwana kamar haka: 08151849417 domin isar da sakon mara gurbi domin a samu nasarar daukan mataki a kansu cikin gaggawa.

Ya kuma bukaci jama’an jihar su mara musu baya wajen yaki da ta’addanci a kowani lokaci, ya kuma bayyana cewar rundunarsu ba za ta taba zura ido wasu na cin karensu babu babbaka ba, dole ne su taka musu burki.

Wakilinmu dai ya labarto mana cewar dukkanin wadanda tsautsayin ta rutsa da su mawaka ne masu adawa da gwamnatin jihar mai ci.

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!