Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

An Yi Garkuwa Da Sakataren Kudi Na PDP Reshen Ekiti

Published

on

’Yan bindiga sun yi garkuwa da Sakataren kudi na jam’iyya PDP na jihar Ekiti, Mr. Kayode Oni hade da kaisa wani wajen dab a sanshi ba har zuwa yanzu.

An rahoto cewar lamarin ta auku ne da misalin karfe 4:30 na yammacin jiya Lahadi, ta kuma auku ne a daidai babban hanyar Efon- Erio da ke jihar Ekiti, a daidai lokacin da Oni ke hanyar dawowa daga Aramoko Ekiti da ke karamar hukumar Ekiti ta Yamma.

Babban jami’in hulda da jama’a na jam’iyyar, Mr Jackson Adebayo, shine ya shaida hakan wa manema labaru a Ado Ekiti a jiya Lahadi.

Ya bayyana cewar ‘yan garkuwa da mutanen sun tuntubi ‘ya’ya da kuma ‘yan uwan wanda suka yi garkuwa da shi di, inda suka bukaci a basu tsabar kudi har naira miliyan 30 a matsayin kudin fansa gabanin su sako shi daga inda suke boye da shi.

“Wadanda suka yi garkuwan sun tuntubi ‘yan uwansa, inda suka nemi miliyan 30 daga wajensu, su kuma iyayen sun nemi basu miliyan daya don su sako musu dan uwa,”

“Yan uwansa sun kai kokensu ga ‘yan sanda a Efon inda suka yi musu alkawarin cewar za su dauki matakin gaggawa kan lamarin,”

“Jam’iyyar mu ba za ta zauna haka nan ba, har sai mun tabbatar ya samu ‘yanci daga wajen wadanda suka yi garkuwa da shi,”.

A tasa fannin, Kwamishinan ‘yan sandan jihar Ekiti Mr Abdullahi Chafe yai musanta zancen ba, bai kuma tabatar da lamarin sace dan PDP ba, a lokacin da aka tuntubesa a jiya Lahadi.

Chafe ya kara da cewa, zai samar wa manema labaru cikakken zance daga baya.

“Yanzu haka ba zan iya tabbatar musu da lamarin ba, domin a yanzu haka bana Ekiti a halin da na ke ganawa da ku. Don haka zan baku cikakken bayani daga baya,” A cewar shi Kwamishinan.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: