Jihar Bauchi Ta Samu Karin Megawatts 130 Na Wutar Lantarki — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Jihar Bauchi Ta Samu Karin Megawatts 130 Na Wutar Lantarki

Published

on


A Jiya ne kamfanin (TCN) ta kaddamar da na’urar Taransifoma samfurin 60 MBA da 132/33KB a jihar Bauchi wanda zai samar da wuta mai karfin  Megawatts 130 a jihar ta Bauchi.

Da yake jawabi a wajen kaddamar da na’urar raba wutar lantarki a jihar, wanda aka sanya a kauyen Gumi, Manajin Darakta kuma shugaban kamfanin, Usman Gur Mohammed ya bayyana cewar yanzu haka jihar ta Bauchi za ta ci gajiyar wuta mai karfin gaske a sakamakon wannan na’urar taransifomar da aka samar wa jihar.

Ya bayyana cewar, irin wannan na’urar tiransifomar an kuma sanya shi a wasu jahohi 18 da suke fadin kasar nan domin inganta sha’anin wutar lantarki.

Ya bayyana cewar gwamnatin tarayya ta sake tsabar kudi har naira biliyan N72 a watanni biyu da suka gabata domin inganta harkar wuta da kuma samar da kayyakin aikin da zai kai ga inganta wannan fannin don amfanar jama’an kasar Nijeriya.

Shugaban TCN ya yaba sosai wa gwamnan jihar Bauchi Mohammed Abdullahi Abubakar a bisa samar da filin da aka sanya wannan na’urar hade da biyan jama’an da suke da mallkin wannan filin kudinsu na hakkin filin da aka amsa a wajensu domin sanya wannan na’urar.

Da yake jawabinsa, Sarkin kauyen Dumi Alhaji Hussaini Muhammed ya roki gwamnatin jihar da ta samu nasarar hade kauyukan da suke makwafta da wannan wajen irin su Gudum Fulani, Rusa da Sabuwar Dumi domin fadada wannan wajen da wutar zai yi aiki a filin domin cin gajiyarsa na tsawon shekaru.

Da yake tasa jawabin, Gwamnan jihar Bauchi Muhammed Abubakar ya bayyana cewar sanya wannan na’urar tiransifomar da TCN a jihar a matsayin wani ci gaba sosai da zai kawo dauki wajen inganta harkar wuta a jihar.

Lauya Abubakar wanda kuma shine ya jagoranci bude wannan injin ya bayyana cewar gwamnatinsa za ta ci gaba da hada kai da wannan kamfanin ta TCN domin fadada harkar wutar lantarki a jihar ta Bauchi da kauyekun da suke jihar.

M.A Abubakar ya bayyana cewar samar da karin wuta har Megawatts 130 zai kawo dauki sosai wa hasken wutar lantarki a jihar ta Bauchi, don haka ne ya bayyana hakan a matsayin babbar ci gaba wa jihar ta Bauchi.

Advertisement
Click to comment

labarai