Connect with us

ADABI

‘Salon So’ Na Hadiza Salisu Shareef

Published

on

Cikin filinmu na Taba Ka Lashe, wanda yake kawo muku gajeren labari ko tsakure daga cikin littattafan fasihan marubutanmu, a yau Lahadi filin zai tsakuro muku labari ne daga cikin littafin ‘Salon So’ littafin da marubuciya Hadiza Salisu Shareef ta rubuta.

Hadiza Salisu Shareef, marubuciya ce da ta dade tana rubutu a wannan da’ira ta rubutu da marubuta,memba ce a kungiyar marubuta ta mata zalla, wato Mace Mutum Writers Association, ta rubuta littattafai da dama wadanda akalla guda Talatin (30).

Fitattu daga cikin littattafan nata su ne:

-Salon So

-Matar So

-Tattalin So

-Sinadarin Masoya

-Kasaitacciyar Mace

Ga dai tsakuren daga cikin littafin Salon So. A sha karatu lafiya:

Jawahir ta ce “To Anti me zai hana marubutanmu ba za su dinga wayarwa mutane kai ba, ko dan sanin irin wannan sirrikan don mata su mallaki mazajensu a hannu, a daina yawan mutuwar aure, maza su daina fita bariki neman matan banza, su dinga tsayawa iya matansu na sunna kawai?” “To ai Jawahir ki gane matsalar da ake samu ita ce, marubutanmu suna iya bakin kokarinsu na ganin sun ganar da yawancin mutane yadda rayuwar jin dadi ta aure take.

To amma kash! Wani abu da ake kuka da shi wai sai a ce suna bata tarbiyyar yara, wai yara kanana suna diban lattattafai suna karantawa, suna ganin abin da bai kamata ba. Gaskiya ni kuma ina ganin ba haka ba ne, domin idan kin ga yarinya ta lalace to dama can lalatacciyar ce. Iyaye suna ina ‘ya’yansu suke fita su shiga gidan amare su rufe kansu suna ganin kaset din blue film ko America, ko Ibo ko fim din turawa da yake bayyanar da tsiraici karara da yadda ake nuna soyayya ta kazamar hanya.

Wasu ma tare da samari suke gani, to me ye ma ba zai faru ba wajen wannan kallon? Wasu yaran ma da ake batawa ba su da wayewar kan da za su yi karatun littafin ake jan su a yi musu fyade, shi ke nan hanyar lalacewarsu ta samu. Wasu yaran rashin kulawar iyaye da rashin sa ido a kan harkokinsu ne yake jawo hakan, wasu kuwa tsabagen kwadayi ne da rashin kamun kai, da zubar da tsantsar darajarsu ta ‘ya’ya mata.

Don haka ban yarda wai karatun laittafi ke sa ‘yan mata lalacewa ba. Saboda duk wata mace da ta san darajar kanta, to in har ta karanta littafi, ina ganin za ta yi kokarin kare mutuncin kanta, ta yi kokarin kai budurcinta gidan mijinta. Saboda ta karanta littafi ta ga yadda daren farko ya kasance ga jarumar littafin.

Mijinta ya same ta a cikakkiyar mace, ta ga irin tarairaya da kulawar da yake ba ta, ta ga yadda ya ke sa mata albarka har da wata dunkuleliyar kyauta da ya yi mata. To a gani na kowacce budurwa za ta yi sha’awar hakan har ta yi kokarin kai budurcinta gidan mijinta. Abu na Biyu ‘yan matanmu za su iya koyon kissa da shagwaba da kalolin girke-girke da yadda ake tarairayar miji.

Za su san abubuwan da suke kara wa mace ni’ima, yadda za su fara tsuma kansu tun kafin su shiga gidan aure. Don in ba a littafin ba babu inda za su samu hakan, saboda al’adar Bahaushe da kunya babu uwar da za ta iya zaunar da ‘yarta ta koya mata wadannan abubuwa don za ta yi mata aure.

Za dai a yi wa ‘ya fada ki bi mijinki ki yi masa biyayya. To kin je kina ta biyayya yana wulakanta ki ba ki san dalili ba. To duk wadannan abubuwa ne da ba kya yi. Amma aure ya samu tattali sai da kissa, shagwaba, ladabi da biyayya, iya girki, iya kwanciya, amfani da turaruka masu kamshi da na tsuguno.

To cikin ikon Allah za a samu zaman lafiya da fahimtar juna a cikin aure…”

 
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: