Connect with us

KASASHEN WAJE

Annobar Ebola Na Ci Gaba Da Kisa A Kongo

Published

on

Ma’aikatar lafiya ta kasar Kongo ta sanar da mutuwar wani kuma yau lahadi wanda ya kamu da cutar Ebola.

An sami Karin wadansu mutane hudu da suke dauke da kwayar cutar ta Ebola a damokaradiyar jamhuriyar Kwango, bisa ga cewar ma’aikatar lafiyar a sanarwar da ta fitar ta baya bayan nan.

Kawo yanzu, an bada rahoton cewa, mutane arba’in da shida suka kamu da zazzabin mai sa zubar jinni tunda aka sami barkewar cutar.

Shugaban kasar Joseph Kabila da majalisarsa sun tsaida shawara jiya asabar su kara yawan kudin da ake kashewa wajen gudanar da agajin gaggawa a kokarin shawo kan cutar Ebola, da zai kai sama da dala miliyan hudu

Idan dai ba a manta ba, rahotannin sun bayyana cewa, an tabbatar da samun wadansu mutane uku dauke da kwayar cutar Ebola a Damokaradiyar Jamhuriyar Kongo, bisa ga cewar ministan lafiya na kasar.

Ministan lafiyan Oly Ilunga ya fada jiya juma’a da yamma cewa, an sami wadansu sababbin kamuwa da cutar mai kisa a birnin Mbandaka, mai yawan mutane miliyan daya da dubu dari biyu, inda aka sami wani dauke da cutar kwanaki.

Mutane arba’in da uku sun kamu da zazzabin nan mai zafi dake haifar da zubar jinni a yankin,inda aka tabbatar goma sha bakwai daga cikinsu suna dauke da cutar ta Ebola, ana tsammani ishirin da daya daga cikinsu sun kamu da cutar ne, yayinda kuma ake kyautata zaton mutane biyar sun kamu da cutar, inji Ilungu.

Hukumar lafiya ta duniya taki ayyana barkewar cutar a matsayin wani lamarin dake bukatar agajin kasa da kasa na gaggawa, sai dai tace hadarin yiwuwar bazuwar cutar a kasar yana da girma. Hukumar lafiyar ta kuma bayyana cewa, mai yiwuwa ne kuma cutar ta bazu zuwa kasashe tare dake makwabta, sai dai tace babu bukatar kafa dokar kayyade zirga zirga a yankin.

 

 
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: