Connect with us

KASASHEN WAJE

’Yan Adawa Sun Yi Watsi Da Sakamakon Zaben Burundi

Published

on

Jagoran ‘yan adawa a Burundi kuma mataimakin kakakin majalisar kasar Agathon Rwasa, yayin kada kuri’a a zaben raba gardama kan sauya kundin tsarin mulki a lardin Ngozi.

Jam’iyyun adawa a Burundi sun ce ba zasu amince da sakamakon zaben raba gardamar da ya gudana ba akan yiwa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima, wanda zai baiwa shugaba Pierre Nkrunziza damar kaiwa shekara ta 2034 akan mulki.

Kakakin gamayyar jami’yyun adawar, Agathon Rwasa ya ce jami’an tsaro sun rika kama masu adawa da sauya kundin tsarin mulkin kafin zaben na ranar Alhamis, zalika jami’an sun kuma yi barazanar kisan gilla ga duk wanda ya kada kuri’an kin goyon bayan sauya kundin tsarin mulkin.

Ana dai bukatar masu kada kuri’a su bayyana ra’ayinsu kan kara wa’adin shugabancin kasar daga shekaru 5 sau biyu zuwa shekaru 7 sau biyu.

Hukumar shirya zaben kasar ta Burundi, ta ce sama da ‘yan kasar ta Burundi miliyan 5 ne suka yi rijistar kada kuri’a a zaben raba gardamar, wanda ake dakon sanar da cikakken sakamakonsa nan da wani gajeren lokaci.

Idan har jimillar kashi 50 daga cikin masu kada kuri’ar suka goyi bayan yi wa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima, hakan zai baiwa shugaba mai ci Pierre Nkrunziza damar kara wa’adin shekaru 14 a shugabancin kasar, bayan kammala wa’adinsa na yansu a shekarar 2020.

 

 
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: