Budurwar Ranar Sallah — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

ADON GARI

Budurwar Ranar Sallah

Published

on


Lokacin da nake  dawowa  daga masallaci,  bayan kammala sallar Idi shekaran jiya. Mun gaisa da wata daga cikin ‘yan’uwa muharramai. Na kuma lura da yadda ita kanta take cike da walwala da farin ciki, wanda na yi zargin lallai ba ya rasa nasaba da yadda ita kanta take jin ta yarda da cewa kwalliyar da ta yi ta kayatar. Sai na ce mata: “Kai mutanen nan, haka kuke tafe kyau yana kwarara a layi!” Nan take kuwa murmushinta ya fadada. Da yake wancan tunanin ya zo min a raina cewa wata ta kara  kyau yau, sai na lura daga wurin duk wadda na saba gani in na gan ta a ranar sai in ga ta dan sauya kamanni. Sannan ne na tuno da maganar da Bahaushe kan yi, cewa “Ba a zaben budurwa ranar salla.” Amma da alama wannan yana cikin salon maganar da ‘ya’yan Hausawan suka cewa “Sami’ina wa asaina.” Domin dai rankatakaf a ranaku ma ba na jin za a sami  wata rana da ake kwalla dangantakar soyayya wadda kuma sau da dama takan zarcewa har aure  kamar ranar sallar. To ina mafita kenan?

Abubuwan biyu duk suna da muhimmanci, wato maganar da Bahaushen  ya yi da kuma ayyukan da ‘ya’yan Bahuashen suke yi wadanda suka yi hannun-riga da da’awar tasa a wannan fanni. Da gaske ne, idan har tsabar kyau da kwalliya ko fara’a da alamun nuna walwalar zuciya ake dubawa ba a irin wannan rana ya kamata a duba kuma a zabi mace don su ba. kamar yadda   kuma ita ma mace, idan magana ake ta kyakkyawan saurayi, ko mai fara’a da saukin-kai da jarumta da budadden hannu da iya tsara zance, to bai kamata ta zabi miji a ranar ba. Sai dai fa wannan bai kamata din ba, ba ya nufin sam kar a yi. A’a, akwai dai abubuwan da suka kamata a yi la’akari da su, bayan wannan ganin da aka yi wa juna a irin wannan ranar da aka fara haduwar, kafin ranar da za a tabbatar da zabin ko akasinsa.

Haka nan, ayyukan da ‘ya’yan Bahaushen kan yi, wadanda kuma ake ganin sun nyi hannun-riga da tasa shawarar, shi ma abu ne mai muhimmanci. Kuma tabbas bai kamata a bar shi don wancan batun ba. domin ai babu wata rana da ta fi dacewa da wannan al’amarin kamar ta. Idan har dangantaka kyakkyawa ake so a kulla ta abokantaka ko soyayya, maganar gaskiya ita ce, duk sun fi kyau da dadi a cikin ranakun da mutane suke cike da walwala da farin ciki. Kusan dukkanin lamuran da suka shafi soyayya har a gidajen auren ma sukan faru ne yayin da magidantan suke cikin nishadi da farin ciki. Wannan yana tunasar da mu cewa ai dama can kulla soyayyar ma mun yi shi ne a cikin irin lokacin da muka jin mu cikin wani hali makamancin wannan.

Yi nazari, yayin da aka ce mace tana cikin damuwa da kunci, kuma lokacin da take ji a jikinta cewa ita kanta ba a shirye take ba. Anya kana ganin idan ma saurayi ya yi mata magana za ta tsaya ta saurare shi?  Ba za ka taba samun mace cikin walwala da sakin jiki da saurayi ba, muddin dai ita a karan-kanta ba ta jin ta a kintse daidai da wannan yanayin da ake bukata. Har yanzu samari da dama ba su fahimci cewa wannan yanayin yana daya daga cikin abubuwan da suka sa idan an je hira wurin budurwa wani lokacin sai ta dauki kusan minti talatin ba ta fito ba.  A tunanin da yawa daga samarin, sai kawai su dauka ai ba ta son su ne. Amma da tana son su ai kamata ya yi tana ji an ambaci sunansu ta fito da gaggawar gaske. Abin da ba su sani ba kuma shi ne, watakila da za ta fito a irin wancan yanayin da take jin ta ba a shirye ba, da wannan hirar ta kasance mafi rashin kayatarwa a gare su.

Balle kuma namiji, wanda shi dama da zarar yana cikin damuwa to ba ya son jin ko da motsin wani a kusa da shi, balle ma a kai ga shi da kansa ya kira ko ya janyo maganar. A baya mun tattauna sosai game da irin wannan dabi’a ta rijalul kahf. Yayin da shi namiji ransa ya baci, sai ya shiga cikin kogo. A ciki ne zai yi shiru ya fara  tunanin ya ya zai bullo wa matsalar. Ba kuma zai fito daga wannan kogo ba har sai ya ga ya samo wa kansa mafita. A irin wannan lokaci ba ya son jin magana ko motsin kowa ko komai a kusa da shi, har sai burinsa na samo bakin zaren waccan matsalar ya tabbata. Amma kafin wannan lokaci duk wani abu da zai ja hankalinsa sawa’un da yawan motsi ko da sauti, to babu shakka  nan take zai zama abokin gabarsa.  Wanda wannan kuma yana daya daga manyan sabubban da suke hada rikici ko da tsakanin miji da matarsa ne. Wato idan har ba ta fahimci shi in yana cikin irin wancan yanayi ba ya son a yi masa magana ko a ce sai ya yi magana ba, to lallai za ta dame shi da son yin hakan , yayin da shi kuma hakan shi zai kai makura wurin tunzura shi.

Kai tsaye dai so muke mu ce yayin da duk ake bukatar a ga namiji yana kula ko tanka ‘yan mata, sai an samar da wani kyakkyawan yanayi wanda yake cikin walwala da sakin-rai da kuma karancin damuwa. Kamar yadda duk lokacin da ake so budurwa ta tsaya ta saurari saurayi, musamman ma sabon saurayi. To ana bukatar ta kasance cikin wani yanayi na farin ciki da walwala da yarda da kanta cewa yanzu daidai take da a gan ta. Sabanin lokutan da take jin cewa idan an gan ta akwai matsala.  Idan kuwa haka ne, tabbas babu wani lokaci da yake samar da irin wannan wannan yanayin ga kowannensu kamar lokacin bukukuwan salla. Don haka ba makawa duk wata da’awa za a yi game da wannan ba za ta taba samun karbuwa a tsakanin samari da ‘yan matan ba.  Amma ba laifi Bahaushe maimakon ya ce kar a yi, ya ce a kula da kyau.

Abubuwan da suka kamata a fada wa samarin su kula, maimakon cewa kar su zaba, suna da yawa, amma ba su kadai ya kamata a ankarar ba, har da matan ma. daga cikin abubuwan da ake gudu a irin wannan zaben akwai  cinikin dan baure:  Wanda za ka ga yarinya fes, an ci kwalliya kamar gaske. Amma ashe kasurgumar kazama ce! Wata ta dunguza wani katon tsumma a kanta, wai shi a-cuci-maza. Wanda samarin kan zata gashin kanta ne, alhali kan kamar gwiwar rakumi yake. Da masu kwambala wata hota wai ita ka-fi-bilicin. Ka ga sun yi fara ko ja jawur, ashe nan bakake ne wuluk.  Har zuwa masu nuna walwala da sakin fuska, wadanda a zahiri tsigalallu ne. Duk ka irin wadannan ba za k aiya banbance su a irin wadannan ranaku masu muhimmanci, kamar yadda in ba a ranakun ba ne za ka fahimce su ba. sai dai fa idan an bi ta barawo….

 

 

Advertisement
Click to comment

labarai