Jirgin Max Ya Fara Jigila A Cikin Nijeriya — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

KASUWANCI

Jirgin Max Ya Fara Jigila A Cikin Nijeriya

Published

on


Hukomomin jiragen Max Air sun kammala shirye shiryen yin fara zurga zurgar a cikin gida Nijeriya, baya ga na aikin Hajji da Umrah wadanda suka riga suka saba da su shekarun da suka wuce.

Mataimakin shugaban kamfanin Bashir Maangal shi ya bayyanawa kamfanin dillancin labarai na Nijeriya, ranar Laraba, a wata hira da ya yi da shi. Inda kuma ya bayyana cewar, kamfanin zai fara zurga zurgar ne tun ranar 2 ga watan Yuli.

Ya kara jaddada cewar shi  jirgi zai fara zur zurga ne ranar Laraba da rana, saboda kamfanin ya nuna sewar ya shirya dangane da komai wanda ya shafi fara zurga zurgar cikin gida.

Bugu da kari kamfanin Max Air din ya bayyana cewar za afara zurga zurgar ne daga Abuja zuwa Lagos, da kuma Kano, sauran kuma manyan garuruwan kamar su Sokoto, Maiduguri, Port Harcourt, da kuma Yola, su kuma zasu biyo baya.

‘’ Da yardar Allah madaukakin Sarki zamu fara zurga zurgar ne ta cikin gida , da kuma daya daga cikin jiragen wanda zai zo Abuja, wanda kuma abin zai kasance ne kamar al’amarin daya shafi gwaji.

Mun kammala zamu ne da ranar 2 ga watan Yuli, da wuraren da za a je guda uku, wato Abuja . Lagos , da kuma Kano.

‘’Daga cikin mako daya kuma zamu kawa sauran jiragen saboda mu fara daga Sokoto, Maiduguri,Port Harcourt, da kuma Yola. Sai kuma sauran suma zasu kasance a gaba.

Ya bayyanawa kamfanin cewar kamfanin ya shirya, dangane da ita fara zurga zurgar, zai kuma yi amfani da du kata damar da ya samu, da kuma bayar da gudunmawar shi akan ci gaban Nijeriya.

Ya kara bayanin cewar shi kamfanin Max Air ya samu  satifiket din shi wato shaidar an anamince ma shi da ya fa gabatar da ayyukan shi, a shekarar  2017 daga Hukuma kula da jiragen sama ta kasa NCAA,  tun kuma daga lokaci ne ya fara harkar shi a Nijeriya, amma kuma abinda ya shafi Hajj da kuma Umrah.

Kamar dai yadda ya bayyana shi kamfanin jiragen yana da Boeing 737-300, 737-400, 737-500, da kuma babba 747-600 da kuma 747-700 wadanda za ayi amfani dasu.

‘’Mu ba baki bane Nijeriya saboda kuwa mun kuma dauki tsaon shekaru goma sha biyar, muna harkar zurga zurgar jiragen sama, sai kuman al’amarin daya shafi Hajj da kuma Umrah shi ma muna da satifiket din shi shekaru goma wadanda suka wuce.’’

‘’Cikin yardar Allah zamu yi iyakar kokarinmu, muma mu taimaka wajen ci gaban Nijeriya, da kuma harkar safarar jiragen sama, za kuma sun  kasance ko wadanne wurare na Nijeriya , nan bada dadewa ba’’.

‘’Yanzu muna jirage uku kasa a Kano, wanda daga can zamu fara harkokin namu, za kuma mu fara da biyu ne, yayin da kuma muke jiran zuwan sauran.

‘’Muna da 737-300, 737-400, da kuma 737-500, bugu da kari kuma akwai Boeing 747-600 da kuma 747-700 wdanda sune muke dasu  a Kano  ahalin da ake ciki yanzu’’.

‘’Muna masaniya akanmatsalolin da ake fuskanta wadanda suka shafi zurga zurgar jiragen sama, shirye kuma muke mu fuskance su.

‘’Mun bi kamar yadda ya kamata da kuma duk wadansu abubuwan da ake bukata, akwai wani aikin da ita Hukumar zata yi, kafin mu fara zurga zurgar.’’.

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!