Ronaldo Ya Bar Madrid Zuwa Juventus — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

WASANNI

Ronaldo Ya Bar Madrid Zuwa Juventus

Published

on


Rahotanni sun tabbatar da cewa dan wasa Cristiano Ronaldo ya bar Real Madrid zuwa Jubentus.

Jubentus, wadanda suka lashe gasar siriya A a kakar wasan data gabata tana kokarin ganin ta kammala siyan dan wasan a wannan satin bayan da tuni dan wasan ya amince da albashin da kungiyar zata bashi.

Ronaldo, mai shekara 33 a duniya ya zura kwallaye 450 a kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid sannan kuma ya lashe gasar laliga guda biyu da kofin Copa Del Rey guda biyu da kuma gasar cin kofin zakarun turai guda hudu.

“Barin Madrid da Ronaldo ya yi ya bar bar tarihi, kuma kungiyar ba zata manta dashi ba sannan kuma shugabannin kungiyar ma haka da ragowar ma’aikatan kungiyar da likitoci da kuma uwa uba magoya baya.

A shekara ta 2009 ne dai Ronaldo ya koma Real Madrid daga kungiyar Manchester United akan kudi fam miliyan 80 kuma a shekarar shine dan wasan dayafi kowanne dan wasa tsada a duniya.

 

An fahimci cewa kudin da aka amince da Borussia Dortmund ya kai fan miliyan £17.66 kuma tuni tattaunawa tayi nisa akan cinikin na dan wasan.

Sabon mai koyar da kungiyar kwallon kafa ta Westham, Manuel Pelligrini dai yayi alkawarin dawo da martabar kungiyar a wannan kakar bayan da kungiyar tasha wahala sosai a kakar data gabata.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!