Connect with us

KASUWANCI

‘Yan Kasuwa Sun Koka: Kan Sake Gina Kasuwar Danmagaji Zariya

Published

on

Ga duk wanda ya san yadda gwamnatin jihar Kaduna ke aiwatar da ayyukan ci gaban al’umma ya san gwamnatin na tsare-tsare ma su ingancin da ke sa duk inda gwamnatin ta aiwatar da wani ko kuma wasu ayyuka, za ka cim ma al’umma na murna kan ayyukan da aka yi musu, ko kuma ake yi musu,wato a karshe sai ka ga mai wasa lafiya shi ma dan kallo lafiya.
Kuma duk lokacin da gwamnatin jihar Kaduna ta tashi aiwatar da wasu ayyukan da za a gani da ido kamar hanyoyi da sauran ayyuka, takan yi tsare-tsare ma su inganci, da ta ke ba kowa hakkinsa da zama zama silar da ke haifar da godiya da kuma sanya albarka ga gwamnatin jihar Kaduna.
Kuma duk lokacin da gwamnatin jihar Kaduna ta tashi yin wasu ayyuka, ta kan jagoranci al’amarin da kanta, ba ta sa wani da ba shi a cikin sahun da ake jan silin mulkin jihar a duk wani batu da za ta aiwatar da abubuwan da ta saw a gaba ba, wato abin nufi, ba ta sa ‘yan karan-kada-miya ga duk wasu al’amurra da suka shafi batun ma su wukar yankar magana ba.
In har gwamnatin jihar Kaduna za ta biya diyya ga wadanda ta yanke hukumcin ratsa hanyoyi ta wasu gidaje na al’umma, ya dace gwamnatin jihar Kaduna ta gudanar da bincike ta ma su wukar magana a karamar hukumar Zariya, domin gano yawan shagunan da ‘yan kasuwar suka gina da guminsu, domin su sami inda za su tsuguna su nemi abincin da za su ci su da iyalansu.
Domin daukacin shagunan da suke cikin wannan kasuwa ta Danmagaji, babu rumfa guda daya da gwamnatin jihar Kaduna ko kuma ma su wukar yankar Magana na karamar hukumar Zariya na shekarun da suka gabata ko kuma na yanzu da suka gina shago daya a harabar wannan kasuwa,tun da ko haka ne, babu wasu dalilai da gwamnatin jihar Kaduna za ta dogara da su, na yin kememen biyan diyya ga ‘yan kasuwar da suka kashe kudadensu wajen gina shagunan da suke cikin wannan kasuwa.
Kuma ya na da muhimmanci ga gwamnatin jihar Kaduna ta lura da cewar, babu rana guda da ‘yankasuwar Danmagaji ko kuma kungiyar ‘yan kasuwa suka zauna da wakilan gwamnatin jihar Kaduna domin tattauna batun rushe wannan kasuwa da kuma batun ginin kasuwar, sai dai wani da ba shi da alaka da sahun ma su hannu a sitiyarin mulkin jihar Kaduna, ya bayyana da bakin hura huta, cewar shi ne dan kwangilar da zai gina wannan kasuwa ta Danmagaji.
Ita dai wannan kasuwa ta Danmagaji, a inda ta ke,a nan ne mazabar jajitaccen dan majalisar jihar Kaduna da ke wakiltar Zariya da Kewaye, wanda har zama na musamman suka da wannan Dan majalisar jihar Kaduna mai suna Alhaji Mohammed Dan’asabe [COKALI], inda ‘yan kasuwar suka bayyana ma sa kukansu da suke sa ran dan majalisar ya kai wannan kuka ga fadar gwamnatin jihar Kaduna, amma har zuwa hada wannan rubutu, babu wani kishin-kishin da ya nuna wannan zaman da kungiyar ‘yan kasuwa suka yi da wannan dan majalisa an kai maganar gaba.
A karshe, yanzu dai ‘yan kasuwar na kukan za su iya tsintar a tsalle guda da za su yi da za su fada rijiya gaba dubu, da za su tsalle dubu ba su fito ba.Wato ke nan a kwai yiwuwar za a yi ma su Sakiyar Da Babu Ruwa Babu Jini, da tarihi zai maimaita kansa.
To tarihi zai maimaita kansa ma na, domin a shekara ta 2013 wani tsohon kantomam karamar Zariya, ya fara gina shaguna a bakin kasuwar Dan Magajin, a ranar da aka fara rushe shagunan da suke wannan kasuwa a shekarar da aka ambata,inda a nan take wasu mutane suka fadi, wasu suka rasa rayukansu, wasu kuma daga wannan shekara, wasu ‘yan kasuwa suka sami matsalar da har zuwa yau ba su fita ba.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!