Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Kotu Ta Yi Wa Sojan Bogi Daurin Shekara 3

Published

on

Wata kotu a garin Minna ta daure wani mutum mai suna Tanko Mohammed dan shekara 32 da haifuwa a gidan yari na tsawun shekara uku domin yaudarar mutane cewa shi soja ne tare da amsar kudadan mutane wanda ya kai naira miliyan 7 don ya shigar da su aikin soja. An gurfanar da Mohammed domin laifuffuka guda hudu wanda suka hada da laifin cin amana, laifin magudi, laifin sojan gona sai kma laifin yaudara.

Lauyan ‘yan sanda mai suna Daniel Ikwoche ya gaya ma kotu ranar Talata cewa, wani mutum mai suna Diko Barde ya taba kai karan shi a ofishin sashin na Minna ranar 9 ga watan Yuli. Ikwoche ya bayyana cewa a watan Maris na shekarar 2017 ne Barde ya kai karan wanda ake zargi, ya zo ya ce masa shi soja ne a rundunar   sojojin Nijeriya take Zariya, kuma an bashi damar yawo mutane 42 a dauke aiki a cikin rudunar sojojin Nijeriya. Ya bayyana cewa, kowani mutum daya zai biya kudi naira 105,000 ko kuma naira 150,000 shi ya kama naira miliyan 7, kuma har yanzu babu aikin.

A cewarsa, bincike ya nuna cewa mutumin da ake zargi yana da wata mujalla na karya wanda aka duga a shekarar 2013 ga wajen horar da rundunar sojojin dake Zariya. Ya ce wannan laifi ne da ya sabe wa sashin na 312, 322, 132 da kuma 217 na dokar Penal Code).

Lokacin da aka karanta masa, Mohammed ya amsa laifinsa kuma yana rokon kotu da ta yi masa sassauci.

Lauyan da yake kare shi ya roki kotu da ta yi masa hukuncin sashi na 157 na kundin tsarin mulki.

A cikin shugancinsa, mai shari’a Nasiru Muazu ya ce, ba za a yi masa sassauci  hukuci ba tunda da gangan ya aikata domi shima ya dandani radadi abin da ya aikata ma wadannan  mutanan. Ya ce, ya daure shi na tsawan shekara daya a gidan yari domin laifin cin amana, laifin magudi, laifin sojan gona sai kma laifin yaudara da ya aikata.

Ya Kashe Dan’uwansa Saboda Naira 800 Kudin Wuta A Abiya

A ranar Talata ne rundunar ‘yan sandar jihar Abiya ta samu nasar cafke wani mutum mai suna Jude Okebuagwu kasamakon kashe Chibuzor Ogbunma dan shekara 56 saboda kudin wutar lantarki naira 800. Al’amarin ya faru ne a gidan wanda ake zargi da kisan cikin kauyen Umuoko a karamar hukumar Ntigh-Umukalu-Isiala-Ngwa dake Jihar Abiya. An bayyana cewa Okebuagwu ya ki biyan kudin wutar lantarki wandan ya kai ga yanke masa wuta. Wannan ne ya bashi yaushi har ya barmaki marigayin da bel mai  kan karfe ya buga masa a kafada.

Kwamishinar ‘yan sandar Jihar Abiya Mista Anthony Ogbizi ya tabbatar da aukuwar lamarin. Ya kara da cewa marigayin shi ne shugaban kauyansu kuma yana cikin kungiyar masu kula da wutan lantarki. Ya ce marigayin ya mutu ne sakamakon raunin da makashin ya yi masa.

Ogbizi ya ci gaba da cewa wanda ake zargi ya amsa laifinsan kuma za a kai shi Kotu.

“Marigayin ya mutu ne sakamakon rauni da makashin ya yi masa kuma wanda ake zargi ya amsa laifinsa sannan za a kais hi kotu domin ya fuskanci hukunci, inji shi.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: