Abin Da Ya Kamata A Sani Game DaMasallacin Ka’aba — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

RAHOTANNI

Abin Da Ya Kamata A Sani Game DaMasallacin Ka’aba

Published

on


A Yanzu Masallacin Harami wato Ka’aba da ke Birnin Makkana kasar Saudiyya shi ne masallaci mafi girma da tsarki a ban-kasa. Shi ne masallacin da ake nunka ladan sallahsau dubu dari fiye da sallah asauran masallatai. Masallacin Harami ne nafarko daga cikin masallatai uku mafi daraja a duniya,da suka hada da Masallacin Annabi SAW da ke Madina, da kuma Masallacin Kudus da ke Isra’ila.

A cikin birnin Makka dakin Ka’aba yake, wandashi ne ginin farko a duniya kamar yadda musulunci yanuna, kuma shi ne Al-Kiblar da Musulmai ke kallo a duk lokacin da za su yi sallah akowace kusurwa ta duniya. A can Makka ne ake cikawasu sharudi guda daga cikin shika-shikan musulunci biyar da ake so kowanne musulmi yasauke idan ya samu iko, wato aikin Hajji, wanda ya kun shi tsaiwar arfah da Dawafi da Sa’ayi tsakanin Safa da Marwa.

Kuma burin kowane musulmi ne ya ziyarci wajenya san yaya wajen yake. Girman Masallacin Girman Masallacin Haramina Makka ya kai murabba’inmita 356,800, kuma yanaiya daukar kusan mutum 800,000 zuwa milyan daya a lokaci guda wadanda za sukasance masu ibada a lokacin aikin hajji ko Umrah, kamar yadda shafin intanet mai kulada masallacin ya ruwaito.

An kawata wannan masallacin da hasken wutar lantarki tarwal ta ko ina, ta yadda dawuya mutum ya gane lokacin faduwar rana saboda yadda aka sanya fitillu masu haskena musamman. Akwai na’urar lifta da dama da ke kai mutane samada saukar da su kasa, daga matakalar bene mai tafiya dakanta ta hanyar amfani da hasken lantarki. Akwai ginin karkashin kasa da kuma wasu hawa biyu zuwa uku da kuma saman masallacin harami da ake ibada a wuraren. An shimfida dadumai ta ko ina a cikin masallacin in banda harabar Ka’aba inda ake zagayawa don yin dawafi, ankuma girke manyan kulolishake da ruwan zam-zam domin mutane su sha a duk lokacin da suke bukata ko bayan sun kamala ayyukan ibada.

Bandaki ko magewayi

An gina magewayi nazamani ta kowacce kusurwarmasallacin haramiu domin milyoyin mutanen da ke zuwa su samu damar zagayawa ba tare da samun cikas ba. Kazalika an kuma ware sashen mata daban, na maza daban. An sanya duk kan kayyakin amfani na zamani da kuma ruwa a kowane lokaci da hasken lantarki ba daukewa, kuma masu aikin tsaftace wajen suna nan badare ba rana. Harwa yau an kuma sanya alamar da ke nuna bandakin maza dabanna mata daban da kumasauran allunan sanarwa cikin harsuna dabam dabam na duniya musamman don masu zuwa zuwa wannan kasa don ibada.

Manyan abubuwan da ke cikin masallacin Harami

A wannan tsarkakakken masallaci akwai Ka’abatul Musharrafa, wato Dakin Allah Mai Tsarki, inda nance alkiblar da duk musulmanduniya ke fuskanta idan suna sallah. Tsawon Ka’abaya kai mita 12, fadinta kuma mita 10 sannan tsawonta ya kai mita 15. An lullubeta da bakin yadi da ake kira Kiswah, wanda yake dauke da rubutun Kur’ani mai girma da aka yi da ruwan gwalkuma duk shekara ake sauya sabuwar Kiswah a dakin ka’abah. Kofar shiga dakin Ka’aba tana daga bangon arewa maso gabashin dakin.

A jikin Ka’aba akwai Bakin Dutse da ake kira, Hajrul Aswad inda daga nan ne ake fara dawafi, kuma ana so mai dawafi ya sumbanci dutsen, in ya samu dama. In kuma bai samu damar sunbataba, sai ya taba da hannu, ko kuma ya nuna shi da hannu in bai samu damar tabawarba saboda cunkoso. Multazam ma wani bangarene na Ka’aba da masu ibadah kan tsaya don yin addu’a. Yana tsakanin dutsen Hajarul Aswad da kofar Ka’aba.

Anaso idan mutum ya samu damaya kara kirjinsa da cikinsa da hannayensa a waje, don haka ake ganin mutane suna dafifia wannan wajen saboda yana daga wuraren amsa addu’a da ake karba nan take wato mustajabah. Fadin wurin yakai mita biyu.

Akwai kuma Makama Ibrahima inda a bayansa ne ake so a yi sallah raka’a biyu bayan kammala dawafi. Anan ne aka ajiye dutsen dake dauke da alamar sawun Annabi Ibrahim AS wanda yataka a lokacin da ya ke ginin Ka’aba. Hijri Isma’il wanda ake kuma kira Hateem wani bango ne a jikin Ka’aba.

An zagaye bangaren sa kuma yana daga bangaren arewa maso yammacin Ka’abah wannan wajen shi ma yana cikin Ka’abah. Kuraishawa ne suka fitarda shi daga Ka’aba lokacinda suka sake ginin dakin. Sun kasa shigar da shi cikin dakin ne saboda rashin kudi. Sun shardanta cewa da kudin Halal kawai za a iya amfani wajen yin ginin, abin da ya jawo ke nan suka rage girman dakin saboda gaza samun isasshen kudin halal domin aikin a wancan lokacin.

Dutsen Safa da Marwakamar yadda Allah ya fada a Alkur’ani mai girma “Lallaine Safa da Marwa suna daga wuraren ibadar Allah, to, wanda ya yi aikin Hajji a dakin ko kuma ya yi Umrah, to, babu laifi a kansa ya yi dawafi tsakaninsu. Kuma wanda ya kara yin wani aikin alheri to, lallai ne wadannan su ne shiryayyu.” (SurahBakara aya ta 158). Daga dutsen Safa ake fara Sa’ayi yana kusa da Dakin Ka’aba, yayin da Dutsen Marwah yake da nisan mita100 daga dakin Ka’abah. Nisan da ke tsakanin duwatsun biyu kuwa mita 450 ne.

Rijiyar Zam-zamna daga bangaren gabas da Ka’aba da nisan mita 20.Wannan rijiya na samarda isasshen ruwan da baitaba kafewa ba tun lokacinda Ubangiji Subhanahu Wa Ta’ala ya samar da ita azamanin Annabi Ibrahim AS, kamar yadda malaman tarihi suka ruwaito. Akwai kofofi biyar wadanda su ne manya manya a Masallacin Haramida sun hada da Kofar Sarki Abdulaziz – Bab Abdulaziz da Kofar Fatahi – Bab Fatah da Kofar Safa – Bab Safa da Kofar Umra – Bab Umrah da Kofar Sarki Fahad – Bab malik Fahad. Sai kuma wasu kananan kofofin kamar Baab Ibrahim da Bab Wedaa da Bab Ali da Bab Abbas da Babun Nabi da Bab Salaam da Bab Ziyarat da Bab Haram da sauran su. Akwai kuma kananan kofofi bayan wadannan, inda idan aka hada su sun zama kofofi 95.Akwai manyan Kubbobi guda hudu da aka gina su akan kofofin Bab Fathi da Bab Abdulaziz da Bab Umra da Bab Safa. Sai kuma kananan Kubbobi 48. Jumullar kubbobin sun kama 52 kenan. Akwai matakalar bene masu amfani da inji guda 56 a baki dayan masallacin, da ake kira Escalator da Turanci. Akwai Hasumaya gudatara a Bab Fahad da BabAbdulaziz da Bab Umra dabiyu a Bab Fath da Bab Safa. Tsawon hasumayoyin sun kaimita 92.

Limaman Haramin Makka goma

Manyan limaman masallacin a yanzu su ne:

  • Abdul Rahman Al-Sudais
  • Saud Al-Shuraim
  • Abdullah Awad AlJuhany
  • Saleh Al Talib
  • Saleh Al Humaid
  • Bandar Baleelah
  • Usaamah Khayyat
  • Yaseer Al Dosari
  • Khalid Al Ghmadi
  • Maher Al Muaikly

Yadda ake wanke masallacin harami da kewaye

A na wanke dakin Ka’abahsau biyu duk shekara. Ana wanketa ne da ruwan da aka hada da turaren oud, da ruwa mai kamshin furrai, da kuma ruwan zam-zam. Manyan shugabannin Saudiyya ne ke jagorantar wankin, tare dawasu shugabannin musulmaina duniya da ake gayyata, ayayin wani taron wanki namusamman da ake yi.

Ana nuna wata irin kwarewa da bajinta wajen wanke filin masallacin, wato wajen da ake dawafi a kasada minti 30. Haka kuma ana wanke duka daben tayil din da ke cikin masallacin da kewaye, da kubbobi, da hasumiyoyi, da durkoki, da gadoji da kuma kofofin masallacin a kullum. Su ma magudanan ruwan da ke masallacin ana wanke su da sabulu da maganin kwari.Wuraren da ake wanke wasun hada da wajen Safada Marwa, da ma harabar masallacin daga waje da kowace kusurwa.

Fadin wajen da ake wanke wa akullum ya kai murabba’inmita 700,000. Sannan idan an kammala aikin fadada masallacin, girman wajenda ake wankewa zai kai murabba’in mita miliyan daya da dubu dari takwas. Shinfidun darduman alfarma da ke masallacin sun kai 30,000, kuma a koda yaushe suna kasancewa tsaf-tsaf gami da kamshi. An kafa wani wajen wanke darduman na zamani namusamman domin wanke shinfidun masallacin kawai. Sau uku ake wanke shinfiduna kullum.

Sannan ana bin matakai har zuwa biyar wajen wanke war. Matakan suna farawa da kade musu kura, da wanke su, da matsesu, da shanya su a rana, sannan a nannade su.

Wuraren alwala da na shan ruwan zam-zam ana wankesu ne sau biyar a kullum. Su kuma bandakai (mekewayi, (bayan gida) da yawansu yakai 14,000 ana wanke su sau hudu a kowace rana. Duk da dubban mutane dake shiga wuraren na ibada, ana wanke wuraren ba tareda an shiga rayuwar masu ibada ba. Sama da mutum 200 ke sa ido domin ganin an tsabtace wuraren ibadar yadda ya kamata. Mutum 27,000 ne ke aikin wanke wuraren na ibada, yayin da mutum 100 ke sa ido wajen ganin an tsabtace wuraren yadda ya kamata. Akwai kuma motoci 40, da motocin kwashe shara 120, da motoci 60 na musamman masu wanke wuraren ibadarda ake amfani da su yau da gobe. Yawan sharar da ake kwashewa yau da kullum takai ton 25, amma a lokacin aikin Hajji da Umara da ake samun karuwar jama’a,yawan sharar yana kai wa ton 90.

Akwai manya manya otal-otal da baki mahajjata ko masu Umra ke sauka wadanda ke daf da wannan masallaci. Acikinsu akwai Darul Tauhidda Zam-Zam Towers da Makkah Hilton da Makkah Millenium da Swissotel Almakam da dai sauran su.Masarautar Saudiyya tana ware miliyoyin daloli domin kula da aikin fadada wannan masallacin da kuma tsaftace shi.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!