Dangote Ya Bukaci A Kara Kaimi Wajen Bunkasa Tattalin Arzikin Afrika — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

KASUWANCI

Dangote Ya Bukaci A Kara Kaimi Wajen Bunkasa Tattalin Arzikin Afrika

Published

on


Alhaji Aliko Dangote hamshakin dan kasuwar a nahiyar Afrika ya yi kira da ayi kokari wajen bunkasa zuba jari a nahiyar Afirka kuma gwamnatoci su kara yin kuzari wajen ciyar da arzikin nahiyar a gaba.

Dangote ya sanar da hakan ne a taron tattaunawa da ake kan gaba da yi karo na biyar na hada-hadar kudi a Birtaniya a ranar Litinin.

Dan kasuwar ya ci gaba da cewa, ci gaban da aka samu na tattalin arzikin kasa da karafa shi ci gaba ne a kasuwar ta Afirka kuma dole ne Afrika ta tashi tsaye ta yi aiki tukuru.

Dangote ya ci gaba da cewa, ya zama wajibi ‘yan Afirka su dinga sayen kayan da ake sarrafawa a nahiyar wanda dama a bisa yarjejeniyar da aka kulla ta kasuwanci a tsakanin kasashen dake nahiyar ake son su kara karfafa kasuwannin dake nahiyar.

Da yake buga misali da halin da ya shiga a baya, Shugaban kamfanin rukunonin na kamfanin na Dangote ya yi nuni da lamarin makwabciyar Nijeriya kasar Benin,wadda take ci gaba da shigo da Siminti daga kasar China, amma kamfanin sa bai wuce kilomita 35 ba daga iyaka ya kara da cewar,“ muna bukatar ci gaba da kasuwanci.”

Dangote wanda ya bayyana cewar, Afrika tana da tattalin arzikin kasa da albarkatun kasa da dama wanda za su ja hankalin masu zuba jari.

Da aka tambaye shi a kan yadda aka sanya sunan masana’antarsa ta sarrafa Siminti a kasuwar shinku ya shedawa mahalarta taron taron da suka hada da, masu zuba jari, manyan yan kasuwa, manyan jami’an gwamnati har da shugagaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo da takwaransa  Ali Bongo na kasar Gabon, cewar mai yuwan sanya ne shekarar 2019 mai zuwa. A cewa sa, dole a hada karfi da karfe don a kammala sanyawar.

Da Editan jarida Financial Times, Lionel Barber ya yi magana a kan matsalar daake fuskanta a kasuwanni kamar kasar Tanzania da Ethiopia, Dangote ya yi watsi da maganar, inda ya ce, manufar mu ita ce mu samar da aiki.

A karshe ya ce, a zamana na mai zuba jari daga Afirka, bana son wani mai zuba jari a nahiyar Afirka ya shiga wata matsala domin bana son a maimaita yar gidan jiya.

Advertisement
Click to comment

labarai