Majalisar Dattawa Za Ta Binciki Badakalar NNPC Na Karkatar Da Kudin Shiga –Saraki — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

RAHOTANNI

Majalisar Dattawa Za Ta Binciki Badakalar NNPC Na Karkatar Da Kudin Shiga –Saraki

Published

on


Shugaban Majalisar Dattawa Dakta Bukola Saraki ya sanar da cewa, majalisar zata tsawaita binken ikirararin Manajin Darakta na rukunonin Kamfanin matatar mai NNPC Maikanti Baru,a kan ya ta faru Kamfanin ya karkatar da ribar da aka samu ta Gas da ta kai Naira 145- nba ko wacce lita daya da kuma farashin PMS na man fetur. Majlisar ta kuma kafa karamin Kwami wanda Shugaban masu rinjaye na Majalisar Sanata Ahmad Lawan yake bincike na zargin Naira biliyan 3.5 na biyan rara kudin mai na NNPC. In za’a iya tunawa, Baru a lokacin da ya gurfana a gaban kwamitin a satin da gabata ya bayyanawa kwamatin cewar, Naira biliyan 1.05 kacal aka samu dagaribar ta NLNG.Saraki, a lokacin ta yake mayar damartani a kan tambayar manema labarai a filin jirgin dake garin Ilorin ya ce, ya samu kiraye-kirayen waya da dama a kan maganar daga wasu yan Naijeriya da suka nuna damuwar su a kan maganar.Shugaban Majalisar wanda ya sanar da hakan a cikin sanarwar da mai bashi shawara ta musamman a kan yada labarai Yusuph Olaniyonuya ya fitar ya ci gaba da cewa, wadanda suka kira wayar sun bukaci son sanin matsayin Majalisar a kan maganar da NNPC ta bijiro da ita a gaban kwamitin da Sanata Lawal yake jagoranta. Shugaban Majalisar ya kara da cewa, bayanin da Mikati Baru ya yi a kan binciken daMajalisar take yi ya kamata a kara zurfafa binciken a gaban Majalisar.Ya ce hakan ya nuna cewar, zargin Shugaban marasa rinjaye na Majalisar Sanata Biodun Olujimi ya gabatar da kuduri a gaban Majalisar a kan amincewa da kashi kudin da Kamfanin ya yi. Saraki ya kara da cewa, akwai abubuwa ma su mahimmanci da ya kamata a yi dubi a kan su.Bayanan da Baru ya yi ya tabbatar da binciken da Majalisar take yi, inda hakan ya nuna cewar, akwai bukatar a gudanar da bincike a kan maganar. Ya bayyana cewar, a lokacin da nake yanke hukunci a kan kudurin da Saanata Olujimi, gabatar a gaban Majalisar, na hakikance cewar muna son mu tabbatar da yin gaskiya da bin doka wajen gudanar da binciken a kan maganar rarar ta mai domin muna son yan Nijeriya su san abinda ake cikin a kan maganar. Acewar sa, a saboda haka ne muka kafa kwamitin don mu nuna kokarin da muke dashi a kan maganar muka kuma yanke shawarar Sanata Ahmad Lawan ya jagoranci kwamitin. Bukola ya ce, mun kuma yi mamaki yadda Baru ya byi ikirarin cewar ribar ta NLNG an karkatar da ita ne ta haramtacciyar hanya wadda ya kamata ne a a tura ta a cikin asusun gwamnatin tarayya don bin umarnin da Majlisar ta baiwa NNPC. Ya kara da cewa, ma’ana idan Majlisar ta yi kira ga NNPC da ta gudanar da aikin na samar da wadataccen mai gay an kasa, ashe Baru a wayo yana da lasisin yin ayyukan sa ta barauniyar hanya da kuma kashe kudin da ba ‘a amince ba dasu ba, yain hakan duk sabawa dokoki ne. Acewar sa, a iya imani na Majalisar ta san ya kamata NNPC ta gudanar da aikin ta yadda ya kamata , musaman samar da mai gay an Nijeriya ba tare da sun sha wata wahala ba kamar yadda doka ta tanadar. Ya kara da cewar, binciken zai bukaci Baru ya gabatarwa da Majalisar amincewar da aka baiwa NNPC ana karkatar da ribar ta zuba jarin da aka yi daga NLNG wadanda kama ya yi a zuba ribar a cikin asusun tara rarar kudin mai na matakan gwamnati uku. A karshe Saraki ya baiwa yan Nijeriya tabbancin baza a yi wata rufa-rufa akan maganar ba,inda ya ce domin yana da kyakyawan yakini kwamatin zai gudanar da aikin sa yadda ya dace.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!