Gwamnatin Kano Ta Mika Takardun Kammala Karatu Ga Daliban Da Ta Dauki Nauyinsu — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Gwamnatin Kano Ta Mika Takardun Kammala Karatu Ga Daliban Da Ta Dauki Nauyinsu

Published

on


Bayan biyan Naira Miliyon N531,275,482.00 daga basukan kudaden Karatun daliban da Gwamnatin Ganduje ta gada daga Gwamnatin data gabata wadanda ke karatu  a Jami’o’i biyar masu zaman Kansu, Gwamnatin Kano karkashin Jagorancin Gwamna  Dakta Abdullahi Umar Ganduje, Gwamnatin Ganduje ta mika shaidar kammala Karatu  ga daiban da suka samu nasarar gama karatunsa nasu cikin nasara tare da samun digirinsu daga Jami’ar  Cresent Unibersity dake  Abeukuta, Jihar Ogun.

Daga cikin Daliban da suka yi hafzi da shaidar kammala Karatun akwai Garba Gambo wanda ya samu shaidar mai matakin na farko a bangaren kimiyyar lafiya, sai kuma Hassan Haladu, Modibbo Muhammad Sulaiman da kuma Maryam Sani wadda ta samu mataki na biyu.

Da yake mika shaidar ga Daliban da suka kammala Karatunsa nasu Mataimakin Gwamnan Kano Dakta Nasiru Yusif Gawuna ya bayyana godiyarsa ga Allah sannan kuma ya jinjinawa iyayen daliban bisa goyon bayan da suka baiwa Gwamnati domin tabbatar da wannan kyakkyawan mafarki na ‘ya’yan nasu.

Gawuna  ya ci gaba da cewa  babban al’amarin da wannan Gwamnati ta fi mayar da hankali akansu  shi ne tabbatar da ganin ana bayar da tallafi ga daliban da ba suda cikakken karfin samun ci gaba da karatu a makarantun gaba da sakandire ko suka kasa samun halartar aikin

yiwabkasa hidima bayan sun kammala diigirnsu.

A cewar Mataimakin Gwamna a kokarin da wannan Gwamnati tayi  na warware wannan matsala, Gwaman Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya bada umarnin fitar da makudan kudade domin biyan basukan  kudaden karatun dalibai ‘yan asalin Jihar Kano dake karatu a Jami’o’i masu zaman kansu.

Gawuna ya kara da cewa yana daga cikin kokarin wannan gwamnati na kara samar da sabon tsarin da zai saukaka ci gaba da warware ire iren wadanan basuka da dalibai ke bin gwamnatoci afadin Kasarnan.

Mataimakin Gwamnan na Kano Dakta Nasiru Yusif Gawuna ya bayyana cewa duk dimbun basukan da aka gadarwa wannan gwamnati, amma Gwamnatin Dakta Abdullahi Umar Ganduje ta sha alwashin ci gaba da daukar nauyin Karatun dalibai  dake karatu a Jami’o’in nan biyar masu zaman kansu Ko a cikin watan da ya gabata na October sai da Gwamnatin Kano ta biya bashin Naira Miliyon N531,275,482.00 wanda ke zaman kashi 50% zuwa karshen watan Nuwambar wannan shekara.

Da yake tsokaci kan basukan kudaden karatun daiban dake karatu a kasashen waje da sauran kudaden abinci da na wuraren kwana wanda suka tasamma Naira Biliyon hudu akarshe kakar karatunshekarar data gabata dukkan Gwamnatin Ganduje ta biya su.

Saboda haka sai Mataimakin Gwamnan ya bukaci daliban da suka kammala digirin nasu da cewa karsu tsaya bata lokaci, su ci gaba da neman digiri harda digirgir domin wannan Gwamnti ashirye take na ci gaba tallafa masu.

Tunda farko data ke gabatar da jawabinta shugabar hukumar bayar da tallafin karatu ta Jihar Kano  Farfesa Fatima Umar ta bayana cewa daga cikin dalibai 1,150 da aka tura karatu jami’o’I biyar masu zaman kansu wadda Gwamnatin baya ta tura, sama da kaso 90% daga cikinsu  yanzu duk sun kammala karatu kuma tuni aka biya dukkan basukan da aka gada daga

Gwamnatin data gabata.

Hakazalik Farfesa Fatima Umar ta ci gaba da cewa Gwamnatin Kano ta biya alawus alawus ga daliban zangon karatu na 2015/2016 wanda ya kama Naira Miliyon 352 wanda aka fitar a watan August na wannan shekara. Kamar yadda kakakin mataimakin Gwamnan Hassan Musa Fagge ya shaidawa LEADRSHIP A Yau Juma’a

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!