Yajin Aiki Da Illarsa A Bangaren Ilimi — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

RA'AYINMU

Yajin Aiki Da Illarsa A Bangaren Ilimi

Published

on


Al’ummar Nijeriya sun fara damuwa sosai kan yadda yajin aiki musamman na Kungiyar malaman jami’a (ASUU) ke dakile ci gaban ilimi a wannan kasa, domin kuwa har ma yana neman ya zama cikin tsarin Kungiyar. Har ta kai ga ana mayar da duk wata matsala da taso tsakanin Kungiyar da gwamnati, ta zama yajin aiki ne hanyar da za a bi wajen ganin an cim ma burin da ake da shi. Yin hakan kuma na dada rage wa malaman jami’a kima a idon al’ummar Nijeriya, musamman wadanda ‘ya’yansu ke karatu a jami’o’in da ake yajin aiki.

Bincike ya tabbatar da cewa, idan aka tattara kwanakin da ASUU ta yi tana yajin aiki daga shekara ta 1999, zuwa wannan lokaci, ya kai tsawon shekara uku.

Ranar 17 ga watan Agusta na shekara ta 2017, ASUU ta shiga yajin aikin na har sai babba ta gani, bayan zaman tattaunawar da suka yi a  Federal Unibersity Of Technology Akure da ke jihar Ondo, sakamakon rashin cika alkawarin da gwamnatin tarayya ta yi musu. Duk da cewa gwamnatin tarayya ta gaya musu cewa a wannan lokacin ba ta da kudin da za ta iya biya musu bukatun nasu. Musamman saboda a daidai wannan lokacin ne aka samu faduwar darajar man fetur a kasuwannin duniya, wanda kuma hakan ta sa tattalin arzikin wannan kasar ya yi kasa.

Haka kuma gwamnatin tarayya ta kafa hujja da cewa lokacin da gwamnatin Marigayi Umaru Musa ‘Yar’aduwa ta daukarwa Malaman jami’ar al’kawari akwai kudin da za a iya ba su. To amma bayan gushewarta sai aka samu canjin al’amura yadda rashin kudin daga gwamnati ya sa ba za iya cika wancan alkawari ba.

Saboda haka muke ganin babbar hanyar da za a bi wajen kawo karshen wannan yajin aiki shi ne, gwamnatin tarayya ta biya wa ASUU wadannan bukatu domin a bai wa dalibai damar ci gaba da samun ‘yancin ilimi a kasa. Kin biyan wadannan bukatu tamkar nuna halin ko in kula ne da gwamnati ke yi, na irin halin da al’ummar kasarta za ta shiga, musamman ta fuskar ilimi. Haka kuma ita ma ASUU ya kamata ta sassauto a sake zama da gwamnati a tattauna domin a kawo karshen wannan yajin aiki da ke hana ruwa gudu a bangaren ilimi. Kuma idan an yi zaman tattaunawar ya zama wajibi ga gwamnati ta tabbatar da cewa, ta aiwatar da abin da suka tattauna a kan nasa. Domin kuwa daga cikin babban abin da ASUU ke koka wa da shi tsakaninta da gwamnatin tarayya shi ne rashin cika alkawari a kan abin da suka tattauna.

Ya kamata kasar nan ta tabbatar da cewa, ta kare mutuncinta, ta hanyar tabbatar da iliminmu na tafiya yadda ya kamata, domin ta haka ne za a samu dalibai daga kasashen waje  su shigo cikin kasa domin yin karatu a fannin ilimi daban-daban, wanda kuma samun hakan na daga cikin ma’auni na tabbatar da nagartar ilimi a duniya.

Baya ga matsalar rashin kammala karatu a lokacin da ya kamata da dalibai ke fuskanta sakamakon yajin aikin  ASUU, haka kuma ana samun afkuwar cin-hanci da yawan karuwar aikata laifuka da rage kimar ilimin Nijeriya da rasa ayyuyka da kuma dagula harkokin tattalin arzikin kasa da jinkirta lokacin masu yi wa kasa hidima da kuma jawo wa dalibai lalaci.

Haka kuma wani abu da ke ci wa al’umma tuwo a kwarya a duk lokacin da ASUU ke yajin aiki shi ne, dukkan wasu aikace-aikace da ake yi a jami’o’i ana dakarta su. Saboda haka dukkan wadannan matsaloli na shafar rayuwar jama’a ne, ke nan ba sai lallai dalibi ko malamin jami’a ko makwabcin jami’a ne ke dandana wa ba, idan ASUU suka shiga yajin aiki, kowa na dandana kudarsa.

Duk da cewa illar yajin aikin ga al’umma tana da yawa, saboda haka  yakan shafe su ta hanyoyi daban-daban. Haka kuma yajin aikin na rage darajar kasa a idon al’ummar duniya, domin yana nuna talaucin kasar saboda ta kasa biya wa ‘yan kasarta bukatarsu ta su yi ilimi.

Sabodahaka,  muke fatan gwamnati ta sake duba kasafin kudin da ake ware wa ilimi. Sannan kuma gwamnati ta tabbatar da cewa, ana bayar da dukkan kaso da aka ware wa ilimin ga inda ya kamata. Kuma ya kamta dukkan masu ruwa da tsaki a kan harkar ilimi su kara kaimi wajen bayar da gudummowarsu ta tabbatar da cewa, an kawar da dukkan matsalolin da suka dade suna hana ruwa gudu ta fuskar ilimi.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!