Connect with us

MANYAN LABARAI

Ku Shirya Wa Yajin Aiki Mai Tsawo –Kungiyar ASUU

Published

on

Shugaban kungiyar malaman jami’o’in Nijeriya na kasa, Farfesa Biodun Ogunyemi, ya bukaci mambobin kungiyar da su shiryawa yajin aiki na tsawon lokaci, bayan da kungiyar ta kasa cimma matsaya a tattaunawar da take yi da gwamnatin tarayya a karo na uku bayan fara yajin aikin sai baba ta gani da kungiyar take yi, inda take bukatar gwamnatin tarayya ta cika mata wasu alkawura da ta mata.

Farfesan ya aike wa duk mambobin kungiyar wata wasika, inda yake shawartarsu da su zama cikin shirin jimawa a cikin wannan yajin aikin da suke ciki, sannan ya ce musu su yi biris da barazanar da gwamnatin tarayya take musu ta hanyar takura shugabannin jami’o’in, inda ya ce musu kada wannan burgar da gwamnatin ke yi ya zame musu wani abu damuwa.

Shugaban ASUUn ya bayyana yadda har yanzu gwamnatin tarayya take ta cika duniya da maganganu marasa tushe, amma a kashin gaskiya babu abinda da ministan ilimi na Nijeriya yake yi wajen ganin an kawo karshen yajin aikin, kusan duk bukatun kungiyar babu guda daya da ministan ilimin ya nuna zai iya samar wa kungiyar da shi.

Wasu daga cikin jiga-jigan kungiyar malaman su ma sun tofa albarkacin bakinsu, inda suke kara karfafa abokan aikinsu wajen ganin sun dake har sai gwamnatin tarayya ta biya musu bukatunsu,saboda a cewarsu wannan fafutika ce da suke yi don ganin sun tursasa wa gwamnati ta inganta tsarin karatun jami’o’in kasar nan da ke fuskantar barazanar lallacewa sosai.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!