Connect with us

LABARAI

Mai Taimaka Wa Gwamna Badaru Ya Yi Murabus Tare Da Sauya Sheka

Published

on

Mai taimakawa gwamnan jihar Jigawa Alhaji Muhammad Abubakar Badaru a harkokin gwamnatoci Barrister Mustapha Kaloma ya ajiiya mukaminsa tare da sauya sheka da APC zuwa SDP.
Kaloma ya bayyana wannan mataki da ya dauka a yayin zantawarsa da manema labarai kan dalilan daukar wannan mataki a jiya a birnin jihar dake Dutse.
Da yake zayyana dalilan nasa, Kaloma ya ce ya fice daga jam’iyyar ta APC zuwa SDP sakamakon a cewarsa bai ga wani ban-banci ba tsakanin tsohuwar jam’iyyarsa da PDP da APC wajen adalci ga al’ummarsu.
Haka kuma Baristan ya kuma ce, “na shiga jam’iyyar APC ne bisa tunanin cewa jam’iyya ce wadda zata tabbatar da ingantaccen sauyi wadda talaka zai san ana mulki kuma zai amfana da ita”
“Sannan na yi tsammanin cewa irin mulkin kama-karyar da jam’iyyar PDP ta share shekaru tanayi a Nijeriya za’a samu sauyi, amma sai yanzu na gano cewa duka kanwar ja ce, domin kuwa babu wani sauyi” inji Kaloma.
Sannan kuma ya bayyana cewa, daga wannan rana ya yi rijistar zama halastaccen dan jam’iyyar SDP bisa fatan cewa ita kadai ce kawai jam’iyyar da zata tabbatar da ingantaccen sauyi wadda talaka zai amfana a wannan kasa baki daya.
Daga karshe ya sha alwashin yin aiki tukuru domin tabbatar da nasarar jam’iyyar ta SDP a kowanne mataki a yayin kakar zabe mai zuwa ta 2019.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!