Connect with us

MANYAN LABARAI

Kotu Ta Yanke Wa Matar Sarki Hukuncin Kisa A Nasarawa

Published

on

Tsawon shekara biyar aka kwashe ana gabatar da Shari’a tsakanin dangin Sarkin Gom-mama, Alhaji Adamu Zubairu, Wanda ake zargin Uwargidansa Malama Amina da laifin kisan maigidanta sakamakon zai yi mata kishiya.
Shi dai Sarkin shekara biyar baya, ya gamu da ajalinsa ne ta hanyar ba shi guba a lokacin da yake shirye-shiryen zuwa daurin aurensa.
A jiya ne wannan badakalar Shari’a ta kawo karshe a gaban Mai Shari’a Aisha Bashir ta babbar kotun Jihar Nasarawa, da ke zamanta a garin Lafia.
Mai Shari’an ta yankewa Malama Amina, hukuncin kisa ne ta hanyar rataya bayan ta same ta da laifin kisan Sarki mai daraja ta daya a Masarautan Gom-mama, da ke karamar hukumar Wamba, wanda shi ne maigidanta.

Da ta ke yanke hukunci, Mai shari’a Aisha Bashir ta ce, masu kara sun gamsar da kotu da hujjoji da suka tabbatar da cewa wanda ake tuhumar ita ta aikata wanan mumunan laifin. Ta sanadiyar tabbatar da wannan laifin ne aka yi mata hukumcin da ya yi daidai da laifin ta, za a kasha ta, ta hanyar rataya.
Wacce aka samu da laifin, Malama Amina, ta kashe Mijin nata ne a shekarar 2013 daganan hukumar ‘yan Sanda suka yi awon gaba da ita zuwa gidan Yari da ke garin Lafia, inda ta kwashe tsawon shekaru tana gudanar da rayuwa a nan Kurkuku.
Amina, daya ce daga cikin matan Marigayin, ta kasance kwararriyar Likita ce, wacce ake zargi da ta yi wa mijinta alura ne mai guba, wanda ya yi sanadiyar mutuwar sa nan take.
Da yake magana a kan hukuncin da kotun ta yanke, Jibrin Aboki, lauya mai gabatar da kara, ya jinjinawa kotun bisa hukuncin da ta yanke tare da bayyana cewar zai zama darasi ga masu sha’awar aikata laifi irin na Amina.
Sai dai, Mista Shekama Sheltu, lauya mai kare wacce ake zargi, ya ce za su daukaka kara zuwa Kotu ta gaba.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!