Connect with us

KASUWANCI

NAFDAC Ta Kwace Kayan Kwalliyan Mata Na Jabu Na Naira Miliyan 60 A Legas

Published

on

Hukumar NAFDAC ta sanar ta kwace jabun magunguna da kudin su ya kai naira miliyan 60 a wata ma’adanar kaya dake a cikin jihar Legas. Bayanun hakan yana kunshe ne a cikin sanarwar da Darakta Janar ta Hukumar Farfesa Moji Adeyeye ta sanya wa hannun a ranar Litinin data wuce. Moji Adeyeye ta ce, an samu nasarar ce bayan da wani da ya damu ya kawo Hukumar bayannan sirrin a kan wuri,inda jami’an NAFDAC dana yansanda suka kai samame a babban shagon da kuma inda ake adana su mallakar wani Mista Nzube a Cibiyar Baje Koli dake Legas. Jami’an sun samu kayan da aka ajiye, da wadanda aka shigo dasu daga waje don sayarwa da kuma rabarwa duk na jabu ne kuma basu da rijista Darakta Janar ta ci gaba da cewa, a kayan na jabu har da kayan kwaliyya na mata na jabu kamar na Allurar yin bilichin Glutathione, kayan gyara jikin mata na gargajiya mai suna (Herbal Skin Doctor Collagen Ampoules), Lansedin Allurar yin bilichin fuska ta Kojic-San da kwalaben B.F.G.F Collagen Polypeptide da sauran su. Ta ce, ana zargin an shigo dasu daga kasashen China, Malaysia, Philippines da Dubai. Acewar ta, manyan motoci biyar dake shake da kimanin kayan kwalluya na mata 56 da basu da rijista da kudin su ya kai kimanin naira miliyan 60 aka kwace daga dakin ma’adanar su. Ta yi nuni da cewa, kayan kwalliyar na iya janyo kamuwa da cututtuka ga matan da suke yin amfani dasu kamar kansa da shafar huhu. Darakta Janar ta kuma yi kira ga kada su gajiya wajen kaiwa Hukumar masu yin kayan na jabu da magungunan don daukar mataki a cikin gaggawa. Ta ce, wannan shi ne kamawar farko da Hukumar ta yi a wannan sabuwar shekarar, inda kuma a 2018, Hukumar an ruwaito ta kwace Kwantainonin Tramadol da kudin su ya kai naira biliyan 193. Farfesa Adeyeye ta sanar da cewa, kwacen an samu nasarar ce tare da hadin gwaiwa da yansanda, Jami’an Kwastam a lokacin gudanar da sintirin hadin gwaiwa na duba Kwantaininun dake tashar ruwa ta Apapa a jihar Legas. Ta bayyana cewa, 23 daga cikin Kwantainonin 80 masu zurfi kafa 40 da Hukumar ta sanyawa ido tun a Nuwambar 2017, suma an duba su a lokacin sintirin jami’an a ranar Larabar ,na Nuwamba 14 da ranar Alhamis, ta Nuwambar ranar 15 dukkan Kwantainonin shake suke da Tramadol. Darakata Janar a karshe ta ce, magance shigo da mugayen kayan maye cijin Niheriya zai kare yawan aikata manyan laifuka kamar fashi da makamai da aikata sauran ta’asa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!