Connect with us

RAHOTANNI

Jam’iyar APC Ce Za Ta Sake Lashe Zabukan Da Ke Tafe A Nijeriya

Published

on

Wani jigo a jam’iyyar APC a jihar Katsina mai suna Injiniya Murtala Abubakar Malumfashi ta jihar Katsina ya bayyana cewa jamiyar APC ce za ta sake lashe zabukan da ke tafe a shekarar 2019.
Injiniya Murtala Abubakar malumfashi ne ya fadi haka ne a garin Malumfashi a ranar Laraba da ta wuce a lokacin da Gwamnan jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya kammala zagaye na kamfen a cikin yankin Funtuwa tare da neman alfarma ga talakawa domin sake samun nasarar lashe zaben gwamnan jihar Katsina 2019.
Ya ci gaba da cewa wajibi ne jam’iyyar APC a Nijeriya jama’a su zabe ta domin gudanar da ayyuka na raya kasa da take zubuwa a dukkan fadin kasar nan ya kara da cewa duk da yake ya gamsu da ‘yan da dubbai na jama’a da suke wo fitar dango a kowace karamar hukuma ta shiyyar Funtuwa domin tarbar Gwamnan jihar Katsina tare da ba shi hadin kai da goyan baya da nuna masa farin ciki gameda aiyukan alheri da yakeyi a duk fadin jihar da kewayenta in ji shi.
Ya kara da cewa jagoran tafiya shugabab kasa janaral Muhammadu Buhari alumar bazasu taba mancewa da mulkinsaba a wajan aiyuka na raya kasa da kiwon lafiya ta lakawa da kare mutuncinsyu a kowane lokaci injishi da fatan shima Allah yacigaba da yimasa jagoranci abisa harkokinsa nay au da kullum.
Ya ci gaba da cewa a kan haka yake al’ummar Nijereiya a ko ina suke su zabi jamiyar APC daga sama har kasa domin ci gaba da samun ayyuka na raya kasa a shekarar 2019.
Sannan ya ci gaba da kira ga matasan Nijeriya da su ci gaba da ba gwamnatin Muhammadu Buhari hadin kai da goyon baya musammnan a cikin lokaci na wannan zabe mai zuwa a kokarinsa na ciyar da kasar nan gabata kowa na fanni in ji shi.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!