Connect with us

RAHOTANNI

Kiwo A Teku: Sabuwar Dabarar Bunkasa Abinci Da Kare Mualli

Published

on

Wannan fassara ce da SABO AHMAD KAFIN-MAIYAKI DA IDRIS ALIYU DAUDAWA suka yi daga shafin FARFESA M.K. USMAN Daraktan Cibiyar Bincike Da Wayar Da Kan Manoma Da Bayar Da Dabarun Noma Ta Jami’ar Ahmadu Bello NAERLS da ke Zariya, wanda ya saba gabatarwa a jaridar LEADERSHIP ta ranar Juma’a. Wannan fassarar an yi ta ne daga irin wannan shafin na LEADERSHIP Friday 11-01-2019, domin amfanin masu karatunmu. Ga yadda Fassarar ta kasance:Daga cikin ilimin da ake koya a darasin geography a makarantar sakandire shi ne, cewa, kusan kasha 71 daga cikin kasha 100 na kasar da muke rayuwa ruwa ne ya mamaye ta, sannan kuma tekuna suka mamaye kusan kasha 96.1 na kasar. Haka kuma akwai ruwa a cikin iska, idan muka lura da yadda turiri ke tashi da koguna ta tafkuna za mu tabbatar da wannan magana. Kankara ma na kunshe da ruwa, akwai ruwa a karkashi kasa, hatta na dabbobi da tsirrai dukkansu akwai ruwa a jikinsu. Duk da haka ba ma iya cin cikakkiyar gajiyar wannan ruwa. Kasa da kasha biyar daga cikin 100 na wanna duniyar da muke zaune ruwa ya mamaye, duk da cewa akwai wataccen rowan da zai mamaye dukkan fadin kasar har ma ya yi zurfin kilomita 2.6 a kasa, idan da a ce an yi duniyar nan mulmularliya kamar kwallo.
Wannan kuwa ya kasance hakan ne saboda kuwa na kiyas ta da akwai da akwai kubik kilomita na ruwa biliyan 1.34 na ruwa a cikin Teku, yayin da kuma ita yadda tsarin duniyar yake da akwai sikwaya kilomita milyan 510 na ruwa. Yadda Allah ya halicci duniyar, shi yasa ta kasance bisa ruwa, sai kuma al’amarin zaizayar kasa wanda yake kara rage karsashin yadda duwatsu suke, wannan abu shieke nuna cewar da akwai ruwa da yawa a duniya, wanda kuma ya kai uku bisa hudu na duniya, miutane suna zama ne a wani dan karamin wuri, sai kuma shi banagare na gandun daji wanda ya kunshi kashi 34, akwai kuma wurin da babu komai kamar sahara shi ya kunshi kashi 14, sai kuma kashin 50 na filaye wadanda ake amfani dfasu wajen al’amuran da suka shafi noma.
Sai dai kuma kuma shi al’amarin gaskiya su filayen da ake dasu kusan an matsa masu idan aka yi la’akari da yawan mutane da suka ta’allaka akan su, saboda fiye da shekaru 100 da suka wuce, kamar daga 1900 zuwa 2018. Idan aka duba kafar htp /www, worldmetres dangane da yawan al’umma na duniya, abin ya nuna daga shekarar 1900 a lokacin an kiyasata yawan al’ummar duniya awancan lokacin ya kai bilyan 1.6. An kuma kiyasta cewar duk shekara za asamu karuwar mutane bilyan 1.9 sai hakan tasa a shekararr 1960 sai ga shi yawan jama’ar duniya ya kai ga fiye da bilyan 3.05. Sai kuma a shekarar 1980 lokacin ne yawan jama’ar ya kai ga biliyan 4.458, sai kuma shekarar 2000 yawan al’ummar ya kai ga biliyan 6.958, sai kuma shekarar 2010 sai kuma yawan jama’a ya kai ga bilyan 7.653 wannan ma watan Yuni ne. na shekarar 2018. Wannan ya nuna ke nan yawan al’umma wanda cikin shekaru 118 yawan al’umma wanda ya fara daga bilyan 1.6 ya kai ga zuwa bilyan 7.6, saboda idan har hakan ta auku a cikin shekarau118, don haka idan aka ci gaba da samun yawan al’umma wanda kuma haka ne zai kasance, nan da shekara ta 2050 yawan al’ummar duniya yana iya kaiwa fiye da biliyan 9.8, wanda kuma ake sa ran abin zai kai bilyan 11.2 zuwa shekarar 2100.
Idan aka dan yi tunani shi yawan filayen da ake dasu na noma zasu iya ciyar da al’umma cikin shekarau masu zuwa kamar 50, 70, da kuma 100 masu zuwa. Dole a kara samun filayen da suke cike da dazuzzuka wadanda za a gyara a kuma yi noma, amma kuma wanda zaio iya smar da gamsuwa cikin dan kankanen lokaci. Da kuma bin duk wata hanyar da za abi saboda a kara bunkasa yawan abinci. Ko kuma su al’umma za su sake yin tunani ne na amfani da kashi 71 na duniya wanda yake ruwa ne, saboda kara wsu ayyukan gona. Kuma minene zai iya shafar muhalli idan har aka yi shi wannan tunanin haka da kuma aiwatar da shi, wadannan tamabayoyin sune suka damu masu bincike da kuma wadanda suke son sabon tsari na samar da kayayyakin amfanin gona abinci. Sune matsalolin da za a iya fuskanta a kokarin da ake yi na na kiwo cikin Teku.
Shi al’amarin noman cikin Teku ya kunshi yadda ake yi noma ne wanda sai an sa Takin zamani, ko kuma yadda idana aka shuka ganyaye zasu yi, ga shi kuma babu iska da kuma kasar da za a yi shuka a kanta. Sai dai ruwan Teku ba kuma maganar yin nom da Fartanya ko kuma wata maganar yin Huda da Galmar Hannu ko kuma ta Sha Nunu,yin noma kamar wanda yake yi noma akan Tudu. Ga kuma shi al’amari na kare su kayayyakin amfanin gonar daga barnar kwari, ko kuma duk wasu abubuwan da zasu iya kawo ma amfanin gonar cikas. Shi noman Teku wani irin noma ne zamani wanda wanda ba kuma ba bukata yake ba, da mutum yasa wani jarin shi ba, kafin ya fara shi noman. yana samun duk wani abinda yake bukata daga Ruwa da kuma Rana, noman shi noma ne wanda yake da daukar hankali saboda akwai abubuwan da zasu burge mai yin shi noman. Babban abinda ake nomawa anoman Teku shine Seaweed wanda shi kuma ana da imanin cewar zai iya bunkasa muhalli, saboda shi yana amfani ne da sinadaran nitrogen da kuma Phosohorous wadanda aka narkar dasu, lokacin da yake amfani dasu. Wadannan su ba sinadaran zasu kasance daga karshe zama illah ga ita Teku ba, saboda kuwa, akwai Carbon diodide wanda shi kuma ta hanyar odidation wanda wani al’amari ne wanda lokacin da a kimiyyance wani sinadari ne aka badawa, wannan kuma ya nuna raguwa ke nan, shi a cikin wannan al’amari du kana samu da kuma rasawa. Bugu da kari kuma shi Sewage ya kunshi Bitamin C fiye da Lemu, hakanan ma yafi madara yawan calcium, Kuma yafi soya beans yawan protein abinda ake amfani da shi wajen noman kifi.
Dangane da shi al’amarin da zai iya shafar muhalli a sanadiyar dabarun kiwon Teku, al’amarin gaskiya akwai irin abubuwan da zasu bunkasa muhalli, wasu kuma su lalata, yayin da kua masu kara daukaka su hakan zai yi, ta hanyar samar da seaweed, yana taimakwa matuka wajen aikin da yake yin a kamo su sinadaran niteogen da kuma phosphorus wadanda ake saki matsayin abubuwan da ba a bukatarsu. Ko kuma suka fito daga akuaculture wadandan ba karamin amfani suke da shi ba, saboda suma suna taimakawa wajen kiwon kifi ta hanyar abincinsu.
Saboda haka a karshen shi al’amarin daya kunshi canjin yanayi shi irin wannan al’amarin daya kunshi odidation wani abune wanda ake ajewa saboda Tekunan duniya, saboda abin zai ci gaba da taimakawa al’ummar duniya ba tare da wata matsala ba. Wannan kuma1 ana iya amfani da yin hakan a matsayin wata hanya wadda za a dawo da martabar Teku, ta hanyar amfani da masa ilimin muhalli. Tambayoyi anan sune ta yaya za a kare Teku da kuma dabbobin da suke cikinta, ita kuma ta yaya Tekun zata yi mana kariya, ta yaya kuma zata samar da abinci, kariya, ayyuka da kuma tsaro ko kuma yadda za atafiyar da rayuwa? duk amsar dai bata wuce yadda za a kula da ita Tekun ba wanda kamar yadda shi wanda ya rubuta kasidar yace ba zai gamsu da hakan ba.
Ita ribar da za a iya samu wajen dabarun noman Teku shine taimakon da hakan ke samarwa, wanda kuma abin ba wai ya tsaya bane wajen abubuwan sha’awa, saboda akwai al’amari samar da abinci koda kuwa kadan ne. Sai kuma Kelps na samar da ton 23 na green da kuma 250,000 na shelfish ko wacce Eka cikin watanni biyar. Bugu da kari kuma Seaweeds yana iya kasancewa wani muhimmin abu wajen maganar biofuel. Wani binciken da aka yi daga wani wuri ya bayyana cewar ana iya samun gallon 2,000 na ethanol daga Seaweeds a ko wacce Eka ta gona, wannan ya nuna ke nan hakan yafi sau talatin na abinda waken soya zai iya samarwa da kuma sau biyar fiye da masara ko kuma dawa. Kelp yana yin girma daga tsawon kafa biyar zuwa goma sha biyu muddin dai ya kai wata biyar, duk kuma abinci yana da kayatarwa matuka. Sai kuma Orysters, mussels da kuma scallops suna suna samar ko kuma sun kunshi abinci wanda yake bada fat kadan da kuma Bitamin mai amfani sosai, senium, magnesium, iron da kuma B Bitamins da kuma Omega 3. Sai kuma su ganyayen cikin ruwan an bincika da kuma gano cewar algae wadanda suka bambanta, kamar kelp suna taimakawa wajen samar da Bitamin daban-daban, sai kuma sinadarin minerals da kuma amino acids tara da kuma Omega 3. Noman Teku wata hanya ce wadda ake noman abinci ta muhalli al’amarin kuma ke taimakawa ta hanyoyi daban daban.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!