Connect with us

WASANNI

Victor Moses Zai Koma Kasar Turkiyya Da Buga Wasa

Published

on

Rahotanni daga kasar Turkiyya sun bayyana cewa dan tsohon dan wasan Najeriya kuma dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, Victor Moses, yana cigaba da tattaunawa da kungiyar kwallon kafa ta Fenerbahce domin komawa kungiyar.
Victor Moses, wanda yana daya daga cikin ‘yan wasan da suka taimakawa kungiyar Chelsea ta lashe gasar firimiya shekaru biyu da suka gabata a lokacin tsohon kociyan kungiyar baya samun buga wasanni a yanzu.
Tun bayan da kungiyar ta Chelsea ta canja mai koyarwa, Mauricio Sarri, dan kasar Italiya, Moses wasanni biyar kawai yasamu damar bugawa wanda dalilin hakan yasa yake ganin gwanda yabar kungiyar.
Kungiyar kwallon kafa ta Fenerhbace dai tana zawarcin dan wasan bayan da a kwanakin baya kungiyar ta bayyana cewa tanason dan wasa irin Moses wanda zai dinga taimakawa ‘yan wasanta na gaba.
Tuni dai kungiyar kwallon kafa ta Chelsea tabawa dan wasan damar tattaunawa da kungiyoyin da suke son daukarsa kuma ya tattauna da kungiyar kwallon kafa gta Fulham a kwanakin baya bayan da tsohon kociyan kungiyar Chelsea, Ranieri wanda a yanzu yake Fulham yake zawarcinsa.
A shekarar 2018, Victor Moses ya sanar da yin ritaya daga bugawa Najeriya kwallo, yana da shekaru 27, kwanaki kadan, bayan kammala gasar cin kofin duniya da Rasha ta karbi bakunci, wadda Najeriya ta gaza fita daga matakin rukuni zuwa zagaye na gaba.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!