Connect with us

WASANNI

Manchester United Ta Na Zawarcin Sabon Ronaldo

Published

on

Rahotanni daga kasar Portugal sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Manchester United tana zawarcin dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Benfica Joao Felix domin ya maye mata gurbin Juan Mata wanda yake shirin barin kungiyar a karshen kaka.
Manchester United tuni tafara shirye shiryen siyan ‘yan wasan da zasu kasance a kungiyar a kakar wasa mai zuwa duk da cewa har yanzu babu tabbacin wanda zai zama kociyan kungiyar na din-din-din.
Sai dai kociyan kungiyar na yanzu, Ole Gunner Solkjaer, shine wanda ake tunanin kungiyar zata baiwa ragamar kungiyar gaba daya sakamakon yanzu yana rike da kungiyar na a matsayin kociyan rikon kwarya.
Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Tottenham, Mauricio Pochettino, da tsohon kociyan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Zinedine Zidane, sune ake ganin daya daga cikinsu zai zama kociyan kungiyar sai dai yadda labarai suke fitowa kungiyar zata iya barwa Solkjaer duba da irin wasannin daya lashe a kungiyar.
Ana tunanin dan wasa Mata baya daya daga cikin ‘yan wasan da zasu cigaba da zama a kungiyar wanda hakan yasa kungiyar tafara neman dan wasa Joao Felix, wanda akewa lakabi da sabon Ronaldo domin maye gurin na Mata.
Felix, mai shekara 19 a duniya ya fara bugawa kungiyar ta Benfica wasa ne a watan Agustan shekarar data gabata sai dai tun daga wancan lokaci dan wasan yaja hankalin manyan kungiyoyi irinsu Real Madrid da Barcelona da Chelsea wadda akace har ta tura wakilanta domin ganin wasan dan Felix a Benfica.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!