Connect with us

LABARAI

Wuta Ta Kone Ofishin INEC A Jihar Filato Kurmus

Published

on

Ana saura sati daya a gudanar da zabe, sai ga wata wuta ta tashi a ofishin hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) a karamar hukumar Qua’anpan dake jihar Filato.
Mr Osaretin Imahiyereobo, shugaban sashen wayar da kan masu zabe kuma jami’in hulda da jama’a na hukumar ne ya sanar da manema labarai haka yau Lahadi a garin Jos wanda ya tabbatar da afkuwar lamarin a daren Asabar.
‘Gaskiya ne ofishin dake Qua’anpan ya kama da wuta saboda sakaci na mai gadin da yake aiki a ranar wanda bai iya sarrafa injin janareto ba kuma yayi korarin kunna shi.’ Inji Mista Oseratin
Ofishin ya kone kurmus tare da duk wasu muhimman abubuwa dake ofishin.
Abubuwan da suka kone sun hada da akwatinan zabe da janareto cike da man fetur da rijistar masu zabe da katinan zabe Wanda ba’a karba ba, da sauran abubuwa muhimmai, inji shi.
Ya kara da cewa sakataren hukumar na jihar, Alhaji Rasheed Gbadamasi tare da sauran manyan jami’an hukumar sun ziyarci wajen domin gane wa idon su abinda ya faru.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!