Connect with us

LABARAI

Gwamna Bello Na Jihar Neja Ya Karfafa Yakin Neman Zabensa

Published

on

A ranar Asabar ne gwamnan jihar Neja Abubakar Bello ya kara karfafa yakin neman zabensa a cocin ‘Ebangelical Church Of Winning All (ECWA)’ da ke Sarkin Pawa tare da bawa tallafin naira miliyan 5 domin sayan filin gina coci a Gwada.
Kamfanin dillancin labarai na kasa ta ruwaito cewa, tun da farko gwamnan ya ziyarci sarkin Pawa Alhaji Musa Mohammed a fadarsa. Gwamnan ya ziyarci cocin ne lokacin mata suke gudanar da taron cocin karo na bakwai. Bello ya bukaci matan su zabe shi a matsayin gwamna tare da sauran ‘yan takarar jam’iyyar APC a babban zabe mai zuwa. Ya yi kira ga matan su yi wa kasar nan addu’an gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali.
“Na yi tunani akwai filin da kuke san siya a Gwada. Na bayar da gudummuwar naira miliyan biyar ta hannun fasto. “Ina rokon ku da ki yi amfani da wannan taro wajen yi wa kasar nan addu’an yin zabe cikin lumana. Muna bukatar addu’a da kuma goyan bayanku domin samun nasara,” in ji shi.
Gwamnan ya umurci kwamishinan kudi da ya bayar da naira miliyan 10 nan take wajen gina sabon fadar Sarkin Pawa. Ya bayyana cewa, gwamnatinsa za ta yi kokarin kawo karshen matsalar tsaro a yankin. Ya shawarci mutane da su tun ga kai rahoton duk wata barazana da suka samu a yankunansu ga jami’an tsaro.
Da yake maida martani, sarkin Pawa ya yaba wa wannan gwamnati wajen kokarin samar da tsaro. Ya yi kira ga gwamnan ya samar da jami’an tsaron yanki wadanda za su dakile ayyukan masu fashi da makami da kuma masu garkuwa da mutane a yankin. Mohammed ya bukaci gwamnan ya samar da likitoci tare da magunguna a babban asibintin Sarkin Pawa da kuma gyara makarantar firamaren yankin.
“Tun da aka maida asibitin zuwa babba asibiti, ba a samar da likitoci ba da kuma magunguna duk da cewa mutanen yankin asibitin suke zuwa. Muna bukatar likitoci tare da magunguna,” in ji shi.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: