Connect with us

RAHOTANNI

Kafin Su Kashe Jami’o’inmu!

Published

on

Sama da kwana Talatin kenan, daliban jami’oin Najeriya, ke zaune a banza babu karatu. Wannan ya faru ne, sakamakon halin ko in kula da gwamnatin Muhammadu Buhari ke nuna ma fannin ilimi, musamman ilimi mai zurfi na jami’a.
Yajin aikin malaman jami’a, bai da bambanci da wanda muka saba gani a baya, wato hakkokin malaman dake taruwa, kuma a nuna ba za a biya ba. Abin mamaki a nan, shi ne,idan a zamanin mulkin soja, da rubabbun gwamnatocin da suka biyo baya, an ki biyan malaman hakkokinsu, to me yasa yanzu da bayin Allah masu gaskiya ke mulki za ai haka? Kada mu manta, wadancan basu iya ba,” azzalumai” ne, shi yasa basu san darajar ilimin jami’a ko malanta ba, to amma wadannan salihai ne, kuma kwararru amma kuma suna haka! A nan an yi abin da bahaushe ke cewa ana zaton wuta a makera, sai kawai a masaka aka ganta.
Wai gwamnati bata da kudin da za ta biya malaman hakkokinsu. Ka ji. To ko can a baya ai haka wadancan gwamnatocin ke fadi cewa ba su da kudin da za su rike ilimi. Amma kuma a wancan lokacin, wasu daga cikin wadanda ke cikin wannan gwamnatin, ciki har da ministan dake rike da ilimin yau, wato Adamu Adamu keta dura ashar da zagi kan wadancan shugabannin cewa karya suke, ba su san yarda za su inganta ilimin ba.
To yanzu su waye makaryata? Su waye mazambata? Su waye basu darajar ilimin ba? Su waye basu san darajar malantar ba? Mu fada ma kanmu gaskiya, ko ba komai, muna da baya, idan suka sayar da ilimin, to shi kenan, talaka zai tashi tutar babu. Burin shi ne, su wulakantar da ilimin, ko su shigo da dibarar da za su nemi da kasuwantar da ilimin da sunan babu kudi, ka ga daga nan, ilimin zai koma sai ‘ya’yansu kawai ke iya samun shi. Wannan ajandar ita za mu duba, mu yak eta, tun kafin su bijiro da ita.
Ina tabbatar maku da cewa, ko bajima ko ba dade, sai sun nemi su cefanar da ilimi a kasar nan, ta yadda sai dan wane da wane kawai za su iya samun shi. Yanzu haka akwai jihohi da yawa a Arewacin Najeriya, yankin da aka tsere mai fintikau ta bangaren ilimin zamani da suka soke bada ilimi kyauta. Ciki hard a biya ma dalibai kudin jarabawar WAEC da NECO. Wasu jihohin duk shekara sai an kai ruwa rana sannan suke biyan kudaden WAEC da NECO din. Duk wannan yakamata da Talakawa su hankalta. Wallahi Kwalta, lantarki, aikin banza ne, idan ba ilimi. Ka gina kwaltar, kuma gina gadojin, darwe daya jahilai su bindige su, kamar abin da muke gani da sunan Boko Haram. Ba tsaro ake fifitawa ba, to ai tsaro na tafiya da wasu abubuwa musamman ilimi. Ta ya za ka dakile rikicin manoma da makiyaya, Bayan da jahilci? Ta yaya za ka dakile rikicin iyaka, rikicin kabilanci, rikicin addini da sauran rikita-rikita bayan da jahilci?
‘ya’yan Talakawa ku daina bari wasu na wasa da makomarku, Wallahi za ku zama bayi na dindindin idan kuka kuskura ku kyale su suka rusa ilimin jami’a.
Ku duba ku gani, kaf din su waye dansa ko ‘yarsa, wannan yajin aikin ya shafa? Amma kuma ranar zabe ‘ya’yansu ko zaben ba za su fito ba, kune bayi, ‘yan zabe za ku zo ku zabe su, kuna cikin yajin aiki, suna kokarin ruguza ku. Ku dubi daliban Nijar mana, akwai wanda ya isa ya taba su? Ku tambayi Yahuza Salisu Madobi, ministan ilimi mai zurfi na kasar ya baku labarin arbatar sad a dalibai. Kudin tallafin karatu kawai aka samu jinkiri, amma duk said a duniya ta ji, amma yau a Najeriya an yi banza da halin da daliban kasar suke ciki, yanda kasan ba su da kowa, basu da gata. Daya daga cikin matsalar daliban Najeriya shi ne, kungiyoyinsu sun zama ‘yan amshin shatar ‘yan siyasa. Cin hanci da rashawa ya yi ma shugabannin kungiyoyin yawa, inda har ta kai yau sai ka ga babbar kungiyar dalibai ta kasa ta rabu gida-gida. Amma a janhoriyar Nijar, duk da bambance-bambancen siyasa, bai sa daliban suka rabu ba. Da sun rabu, to da azzaluman kasar tuni da sun gama da su kamar yadda aka gama da takwarorinsu na Najeriya.
Wai ba kudin da za a gudanar da jami’oin gwamnati. E lalle, tunda muna da jami’oi masu zaman kansu, inda ‘ya’yansu da jikokinsu da matansu da ‘yan uwan matayensu da kilakansu ke karatu , ba mamaki dan sun ce haka.
Yayinda a manyan kasashe inda ma ake mulkin jari hujjar na bugu-da-kari, jami’oin gwamnati na samun tagomashi fiye da na masu zaman kansu, munan inda ake son bautar da mutane abin ba haka yake ba. Kullum dalilai na banza da na wofi za ka ji ana kawowa wai sune yasa ba a iya rike jami’oin. In ma banda rashin tunani da rashin kishin kasa, da kuma manufar cutar talaka, ta yaya wani wai zai ce basu da kudaden da za su biya hakkokin malaman jami’a? Dama bai dauki jami’ar da muhimmanci ba. Kasan idan abi bai cikin tsarinka, to ba dole bane ka bashi hankalinka. Yanzu da yake gina layin dogo ya fi ilimin jami’a, ba har kasar Sin suka je suka ciyo bashi ba?
Don haka dole mu goyin bayan gwagwarmayar da kungiyar ASUU k eta faman yin a ganin a kare jami’oi mallakar gwamnati. Talaka ya fi ka marawa ASUU baya da ka mara ma gwamnati baya, ko banza ASUU nada kyakkyawan kudiri, amma idan ka amince ka mara ma ‘yan siyasa baya, wadanda karya alkawali wurinsu ba wani abu bane, karya da yaudara wurinsu ba wani abu bane, to ga fili ga mai doki, kawai zan ce.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!