Connect with us

LABARAI

An Bankado Shirin Kawo Cikas Ga Zabe A Jihar Kwara

Published

on

Darakta Janar na kwamitin yakin neman zaben tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar, kuma dan takarar jam’iyyar PDP a zaben dake tafe na watan Fairairu 2019, Dakta Ali Ahmad ya bayyana cewa, sun bankado wani gaggarumin shirin da jam’iyyar APC take yi na amfani da wasu shugabaninn manyan makarantun don kawo cikas musamman a mazabar Majalisar Dattijai na Kwara ta Tsakiya, inda za a ayyana sakamakon zaben da cewa, bai kammalu ba, daga nan sai a shirya yadda za a mured gaba daya.
Ahmad, wana kuma shi ne shugaban majalisar dokoki na jihar Kwara ya ce, bayanan na sirri dake a hannun ofishin yakin neman zaben su ya nuna cewa, jam’iyyar APC ta zabo wasu Malaman manyan makarantau in da hukumar zabe za ta nada su a matsayin manyan jam’ian hukumar ta yadda za a yi amfani da su wajen aiwatar da shirin yin magudin.
Ya kuma kara da cewa, “Ministan yada labarai, Lai Mohammed ne a kan gaba wajen ganin an aiwatar da wannna shirin, inda jami’an zaben za su haigar da tashin hankali a runfunar zabe daga nan sai a sanar da sakamakon zaben shugaban kasa tare da ayyana rashin kammaluwar na matakin Majalisar Dattijai a wasu ayyanannun mazaba.”
Ya ce, manufar su shi ne samar da yanayin da zai zamana za a sake zabe a mazabar Kwara ta Tsakiya, ta yadda jami’an tsaro za su shigo su yi dumudumu tare da yi wa masu jefa kuri’a barazana.
A kan haka ne, Ahmad ya bukaci musamman shugaban hukumar dabe na jihar Kwara, Malam Attahiru Madami, da ya tabbatar da ya tantance tare da kuma sanya ido a kan jami’ansa a lokuttan zaben dake tafe.
Daga nan kuma ya mika goyon bayansa ga kiraye kirayen da ake yi ga shugaban rundunar ‘yan sanda Nijeriya, Mohammed Adamu da ya gaggauna sauya wa kwaminshinan ‘yan sanda ja jihar, Kayode Egbetokun wurun auiki saboda samun ci gaba da zaman lafiya a sassan jihar.
Ya kuma kara da cewa, a matsayinsa na jami’in tsarin jagoran jam’iyya APC, Bola Tinubu, a saboda haka babu yadda jihar Kweara dake a karkashin jam’iyyar PDP za ta aminta da sabon kwamishinman ‘yan sanda.
A wata sabuwa kuma, gamayyar kungiyoyin ma’aikata na jihar Kwara sun ayyana cikakken goyon ga jam’iyar PDP a daidai lokacin da ake tunkarar babban zaben kasa tare da fara wad a dzabe shugaban kasa dana majalisar tarayya a ranar Asabar 16 ga watan Fabrairu 2019.
Maia’katan sun bayyana goyon bayan nasu ne ga dukkan ‘yan takarar ja’iyyar PDP a zaben dake tafe a taron da gwamna jihar, Alhaji Abdulfatah Ahmed ya jagoranta a garin Ilori ranar Litiini.
Cikin wadanda suka halarci taron hard a dab rataarar kujerar gwamna na jam’iyyar PDP, Hon. Razak Atunwa tarebda wasu manyan ‘yan jam’iyyar a jihar.
A jwabinsa, Gwamnan jihar, Ahmed ya bayyana shirin gwamnatin jihar na fara aiwatar da biyan mafi karancin albashi na naira 30,000 ga ma’aikatan jihar.
Ya kuma bayyana cewa, gwamnatinsa ta fara biyan bashin albashin wata daya ga ma’aikata da ‘yan fansho na kananan hukumomi da na jihar gaba daya.
Kungiyoyin ma’aikatan da suka samu hakartar taron sun hada da ‘Nigeria Labour Congress (NLC)’ da ‘Trade Union Congress (TUC)’ da ‘Joint Negotiations Council (JNC)’ da sauran kungiyoyin kwadago a sassaan jihar, sun kuma yanke hukuncin goyon bayan dukkan ‘yan takarar jam’iyyar PDP a zaben 2019.
Wadana suka sanyan hannu a kan takardar yarjejeniyar sun hada da Yekini Agunbiade na (NLC) da Nasir Olumo na (TUC) da Salihu Sulyman na (JNC) da Toyin Salihu na (NUT) da Yusuf Salihu na (NULGE) da kuma Seidu Oladimeji na kungiyar (NUP).
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: