Connect with us

WASANNI

Manchester United Za Ta Tabbatar Da Solkjaer A Matsayin Kociyanta

Published

on

Rahotanni daga kasar Ingila sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Manchester United tana dab da tabbatar da Ole Gunner Solkjaer a matsayin sabon kociyanta na din-din-din a karshen kakar wasa.
Tun bayan da kungiyar ta tabbatar dashi a matsayin kociyanta na rikon kwarya, Ole Gunner Solkjaer ya lashe wasanni 10 cikin wasanni 11 daya jagoranci kungiyar ciki har da wasannin FA cup.
Wasu rahotanni daga kasar Norway sun bayyana cewa shugaban gudanarwar kungiyar, Ed Woodward da wakilin masu kungiyar Abram Glazer sun tattauna da wakilin Solkjaer, mai suna Jim Solbakken bayan wasan da kungiyar tasamu nasara akan Fulham.
An bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta bayyana cewa zata tabbatar da Solkjaer a matsayin kociyan ta na din-din-din amma bazata bayyana ba sai an kammala kakar wasa ta bana.
Masana wasanni dai sun bayyana cewa Manchester United bata da niyyar kin tabbatar da Solkjaer a matsayin kociyan ta sakamakon yadda kociyan ya dawo da martabar kungiyar ta hanyar canja yanayin buga wasannin kungiyar.
Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Tottenham, Mauricio Pochettino da tsohon kociyan Real Madrid Zinedine Zidane sune ake zaton kungiyar zata zaba domin zama kociyanta sai dai sakamakon nasarar Solkjaer yasa kungiyar ta canja shawara.
Manchester United zata fafata wasa a yau da kungiyar kwallon kafa ta PSG a wasan zagaye na farko na gasar cin kofin zakarun turai a filin wasa na Old Trafford wasan da ake ganin idan Solkjaer yasamu nasara zai kara sawa kungiyar ta sake yadda dashi.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!