Connect with us

TATTAUNAWA

Abubuwan Da Buhari Ya Kamata Ya Mayar Da Hankali A Wa’adinsa Na Biyu – Dakta Jamilu

Published

on

Dakta Jamilu Nasir Bebeji Shugaba ne a cibiyar samar da magunguna ta addinin Musulinci ta Alyusra, kuma mai lura da al’amuran yau da kullum, da fashin baki a Nijeriya, a cikin tattaunawarsu da wakilin LEADERSHIP A Yau Juma’a, ya tabo batutuwa masu mahimmanci, ciki har da yadda ya kamata Shugaba Muhammadu Buhari ya mayar da hankali a wa’adinsa na biyu, ga dai yadda tattaunawar ta kasance.

Malam me za ka bayyana game da zaben shugaban Kasa na 2019 da ya gudana a Nijeriya?
A uzubillahi minasshaidanirrajim. Bismillahirrahmanirrahim. Wassalatu wassalamu ala Rasulillah wa’ala alihi wasahabihi waman walah. Bayan haka ‘yan’uwa ina yi mana sallama irin ta addinin musulinci, Assalamu alaikum warahmatullahi ta’alah wabarakatuhu.
Ina mika godiyata ga Allah Subhanahu wata’alah kan cin wannan zabe da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi, sakamakon a fahimtar mu da ma shi muka fi so Allah yaba wa, shi ya sa muka yi ta yin irin wannan bayani a baya, ba don komai ba, sai don dalilai da muka sha gaya wa mutane na kokarinsa na kwatanta tsoron Allah, dakuma nuna tausayinsa ga jama’a, da kuma fadi da muka yi a baya kan cewa, in da a ce yana dawata illa da yake da ita kwakkwara ta zaluntar jama’a, to ina ganin cewa, daga yadda ake kokarin tade kafarsa, da dole wannan abu sai an yada shi kowa ya ji shi.
Tun da har makiyansa ba su iya fitar da wannan bayani karara a hujja ba, ya tabbata cewa babu din ne. To kuwa irin wannan mutum da yake da jajircewa wajen ganin ya karbi hakkin jama’a daga duk inda yake ya kuma sada su ga jama’a din, ashe ka ga yana tausayin mutane ke nan. Shi ko duk wandayake da tausayin mutane, to Allah ma yana tausayinsa, Allah Ta’alah yake cewa; ‘’ Wanda ba ya jin tausayin mutane, Allah ma ba ya jin tausayinsa.’’ Tausayi yana cikin dalilai na samun nasara da kuma samun daukaka a duk abin da kake yi, da kuma samun rabo a gobe kiyama.
Ba za mu manta da Hadisin Manzon Allah SAW da yake ba mu labarin wata karuwa da shayar da kare ruwa, Allah Ubangiji ya yafe mata, kuma ya sa a gigdan aljanna. To in dai za a tausa wa abu mai hanta, mutum ne shi ko dabba, ya kasance wannan ya zama sanadiyya da Allah zai maka rahma, ina kumaa ce ka yi da nufin ka zalunce shi ko ma ka zalunce shi din, kuma b aka biyo hanyar tuba ba? to mu a wurinmu, ba wani dalili da zai hana shi cin zabe ko wane iri har abada, sai fa in ya canja daga halinsa da yake kai, wanda kuma a shekarunsa da yake kai a yanzu yana da wuya ya canja din. Duk wanda ya ginu a kan wahli har ya kai shekara 40 yana kai bai canja ba, balle kuma maganar shekara 80 ake yi, ka ga ana maganar ya ninka a kan 40 din, to wannan me yake nema da zai canja a wannan shekarun nasa.
Saboda haka Alhamdulillahi Allah ya tabbatar mana da zatoda muke yi da kuma hasashen da muke yi na cewar zai ci zabe kowane iri ne. duk wadanda suke tsayawa takara mun gaya musu, muka ce da su, na farko dai muna son mu gaya musu su makiya Nijeriya ne, na fadi wannan, duk wanda ya tsaya takara da Muhammadu Buhari bayan ya san da wadannan halaye nasa to shi makiyin Nijeriya ne.
Damin idan muka ce mutum shi matashi ne ya zo shekarunsa ba su kai 40 ba, bai taba rike wani mukami ba, bai taba rike wani abu na Gwamnati ba, yake da ra’ayin shi ma ya zo yaba da gudummowa, ya fadi halayyarsa, ya fadi tarihinsa, kai ya ma fada karara cewa ni na zo na ba da tawa gudunmawar zan yi aiki irin na Buhari, ko kuma wata kila zan zan haura shi ba da yaw aba, to wannan ya yi wa kansa adalci.
Domin su wadannan da suke tsayawa takarar na da shi, mafiya yawancinsu za ka ga sun taba rike wani mukami a Nijeriya an dama da su shekara da shekaru, musamman yanzu shi Atiku Abubakar, ta yaya wanda gashi a jam’iyyar wadda it ace jam’iyyar da tafi karfi a baya, da shi su kai takara da Muhammadu Buhari, shi suka tsayar. Kuma ni ban taba ganin mutumin da aka tsayar da shi takara mtane ba sa son ba irin Atiku. Amma yanzu abin da ya sa ake sonsa saboda ana cikin yanayi na rashin kudi, ya fi da kudi, kuma a yanzu in dai zka fito da kudi, to ko za ka rike bindiga sai an zo an karba.

To amma ‘yan jam’iyyar adawa suna ganin zaben bai inganta ba, domin a wasu wuraren an yi fada ba a yi zabe ba, sannan kuma a wasu wuraren da suke da karfi an soke zabukan, sannan wuraren da ake rigima sun kawo kuri’un da sun fi in da ba a rigima yawa, ya kake kallon wannan batu?
Allah ne fa ya ce, ‘ Wakanal insanu aksara shai’in jadala’mutum shi ne ya fi wata halitta da ka sani jayayya da taurin ka. Yanzu misali Amurka zai je, ana maganar ba zai iya zuwa ba, sai ya shiga cikin jami’an tsaron Bukola Saraki, kowa ya gan shi da kaya irin na jami’in tsaro, ya shiga cikin kariyarsa, wannan abin fa kowa ya gani, yin hakan ba ha’inci ba ne?
Amma shi Shugaban Majalisa ya fito ya karyata hakan ya ce Atiku ba a matsayin hadiminsa ya bi shi Amurka ba
To ai shi ma ba gaskiya zai fada ba, shi ga ai jama’arsa sun ki shi, ba maganar da nake maka ba kenan? Ai in dai kana da mummunan hali sai ka ga ka wulakanta. Ai yanzu ga shi shi ma ya fadi, gashi nan ana yada bidiyon ni an kawo min na gani, tun lokacin da suka kada kuri’a suke tsalle suna murna su san sun kada shi kawai.
To me ya kawo wannan? To mutumimn da ka yi mulki shekara takwas, amma mutane suna nuna maka irin wannan bakar kiyayya wadda ya kamata a ce sun manta da abin da ka yi, suna yi maka kallon mutumin da bai da dattaku da rashin kima. Jama’arka suna farin ciki sun fitar da kai daga wakilcin da kake yi musu. To wannan shi ne zai fadi wata magana mu yarda da ita? Ai ba cewa zai yi Allah daya ba ne babu wata magana da Bukola Saraki zai fada mu yarda da ita.

To a matsayinka na mai fashin baki kan al’amuran kasar nan, sun bayyana zaben nan bai inganta ba, ya kake kallon abin?
Shi ya sa nake gaya maka kuri’ar na ma da ka ga sun samu, ina tabbatar maka da cewa akwai abin aka yi aka same ta Allah bai tona masu asiri ba, amma babu yadda za a yi a samu wannan kuri’a.
Atiku ya yi kankanta, a matsayi a gogewa ya fishi a sanin jama’a a duniya ya fi shi, talakawa da suke sonsa tsakani da Allah ya fi shi, sannan idan gogewa a siyasa ya fi shi, hankali ya fishi, sanin ya kamata ya fi shi. wato Atiku da PDP sun nuna toshewar basira, hakan ya nuna Allah yana son ya kwato hakkin talaka, tun da ko kudin da suka bayar a zaben fid da gwani, to ko wannan dala dubu goma-goma da raba kana ganin ba zai ishi wani jari ba? tunda yanzu wanda aka ba shi zai je ya kafa jari, to ka ga in haka ba ta ina Atiku zai ce zai yi takara da Buhari, har ma zai ce an yi magudi? Kai hatta kyan fuska ya fi shi.

A cikin bayananka ka nuna a kuri’un ‘yan adawa a kwai rufa-rufa, kana nufin kenan an samu magudi daga gare su ke nan?
To ai ka ga in har ya tabbata hakan an yi tunda ni ban gani da idanuna ba, na ji an ce a nan A.Y.A an kama akwatinan zabe wadanda har ma na daddangwala har guda 12 kuma duk PDP aka dangwala wa, to idan za a kama wannan, ka ga wanda aka yi ba a gani ba ya fi yawa, kenan ka ga an yi yawa ke nan.
Sannan akwai wasu wurare da na gani a labarai, in har ta tabbata ga shi nan an kama wata ‘yan NYSC ga ta nan da hotonta a jeji da kayan bautar Kasa tana dangwala wa PDP. To duk irin wadannan abubuwan la’alla ta haka ne suka samu, ba ka rasa mutanen kawai da suke neman kade wa jama’a wannan ni’ima ta mulkin Muhammadu Buhari, tare da yunkurin sai an yaki wannan ni’ima.

Yanzu Muhammadu Buhari ya sake lashe zabe a karo na biyu, me kake ganin yakamata ya mayar da hankali a kai musamman yadda wasu ke ganin an dan yi kura-kurai a baya?
Gaskiya ne akwai kura-kurai da aka yi a baya, saboda shi dama dan’adam tara yake bai cika goma ba, abin da ake so dai a ce daidensa ya fi kuskurensa yawa, to tabbas Buhari daidensa ya fi kuskurensa yawa.
Yanzu dai addu’ar da za mu yi ita ce, Allah ya ba shi ikon gyarawa,domin na tabbatar ya fi mu sanin cewar ya yi kuskure. Bayan gyare-gyaren kura-kuran baya shi ne, yadda ya taho da ayyuka na inganta hanyoyin nanda wutar lantarki, da kuma harkar tsao din nan, to wannan yaninka kokarinsa ninki goma, a samu hanyar da ba a taba samun irinta ba, a dade ana mafanarta, yadda har jikokinsu idan sun zo su ce wannan aikin Buhari ne, a samu wutar lantarki ya zamto ta inganta.
To idan aka yi haka gaskiya ya zamto ya samar da wuta kafin y agama mulkinsa, wannan na daga cikin abinda zai kara tabbatar da cewa an ga canjin a bayyane, amma idan aka ce ana dauke wuta ta tsahon awa daya ko awa biyu, to har yau dai muna nan ba mu je ko in aba, ka ga ba aga canji ba kenan. Sannan akwai kuskuren da muke yi wanda dole sai nay i maganarsa, wanda kuskure ne suka yi, sun sanar wa da jama’a cewa a watan Disamba za su kaddamar da sabon jirgin sama basu yi ba, basu kuma firo sun yi bayanin dalilin abin da ya hana su yi wannan kaddamarwa ba, kuma an nuna sunansa da hotonsa ‘Nigeria Airways’, ko dai bashi ya fada da makinsa ba, amma dai ai ministocinsa sun fada, kuma na sa rai, domin ina alfahari da kasa ta Nijeriya.
Yanzu zan je Umrah zan fi so a ce jirgin “Nigerian Airways” zan hau, ka gazan yi murna, kuma zai zama ba a bin bakin ciki ga makiyansa, ya zama bin da ake ganin ba zai yiwu ba, jirgin Nijeriya a ganshi a sama, ai wannan magana ta zama tarihi har abada.
Sannan ya kula da wadanda suke sonsa sosai ya taimake su fiye da yadda ake tsammani, wannan ba laifi ba ne, domin tun da suna sonsa suka kara karfi, to ashe akwai tunanin suna da gaskiya ke nan, ya yi adalci ga kowa, ya samar da jindadi ga kowa, ya bayar da mukami ga duk wanda ya cancanta, wanda yake da kwarewa a ko wace kabila yake, a ko wane addini yake. Amma kuma akwai karfi, misalin wane masoyina ne bari na karfafe shi sosai, saboda zai taimaka min wajen kaza, domin yana daga cikin abubuwan da matarsa ta yi dan tsokaci kansa a baya, cewa to ga fa su wane, ai wane yayi kaza, ai wane masoyinka ne.
To gaskiya ya kamata ya dan dawo da hankalinsa ko yaya yake kan wannan gefen ya kalla, na tabbata wadannan kalaman da nake yi ya fini lura da su ya fi ni basirar gane abin da yake kunshe a mulki, idan dube su zai fahimci abin da nake nufi in sha Allahu.

To Akaramakallah kai dan asalin Jihar Kano ne, ya ka ga zaben a Jihar Kano?
Zabe a Kano ya yi kyau, ko da yake na san za a dan samu matsala a kan maganar tsaro da wasu abubuwa, amma dai ai ya kamata a ce kuri’ar da muka samu ta fi haka, saboda dama Kano ta Muhammadu Buhari ce, ai ni shi ne ma, nake mamaki da Kwankwaso ya dauko wai Atiku ya kawo shi Kano. Kana neman jama’arka su zo ka zo ka dauko mutumin da jama’a ba sa so ka ce za ka tallata shi? ashe hakan ya nuna kai ba mutumin kirki ba ne ke nan kai ma ba ka zabi cancanta ba.
To Akaramakallah mun gode
Ni ma na gode.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!