Connect with us

LABARAI

An Kashe ’Yan Sanda Hudu Ciki Har Da DPO A Jihar Edo

Published

on

A ranar Talata ne a yan bindiga suka kashe ‘yan sanda hudu a ofishin yan sanda na garin Afuze dake jihar Edo. Garin Afuze ne baban hedikwatar karamar hukumar Owan East ta jihar Edo. Cikin wadanda aka kashe a kwai wata ‘yar sanda mai mukamin Sajan kuma tana dauke da ciki, an kuma bayyana sunan ta Justina, haka kuma an kashe DPO da DOC da kuma wani dan sanda a ofishin.
Bayani ya nuna cewa, ‘yar sanda da aka kashe ta samu canjin aiki ne daga garin Benin zuwa Afuze, tana kuma bakin aiki ne a yayin da yan ta’addan suka kawo harin.
Yan ta’adda sun jefa bam ne a ofishin DPO din ne daga baya kuma suna harbe saura jami’an ‘yan sandan dake aiki a ranar.
Bincike ya kuma nuna cewa, an yaudari DPO ne da cewa, yana a baki a wajen aiki, don ya dawo kuma ba a dade ba aka kawo harin.
An kuma bayyana cewa, yan ta’addan na dauke da muggan makamai sun kuma bude dakin ajiye masu laifi inda suka salami dukkan masu laifin dake ciki.
Mutum uku daga cikin wadanda suka gudun sun kuma shiga hannu a yayin da suke tserewa.
Haka kuma wadanda ake zargin sun kai hari ofishin INEC na garin Afuze, inda suka kona motar Hilud na ‘yan sanda.
Da aka tuntube shi don karin bayani, kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Mista Hakeem Odumosu, ya bayyana cewa, yana Abuja don aikin zabe, har sai ya dawo kafin ya iya yin bayani a kana bin da suka faru.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!