Connect with us

SIYASA

Mata Sun Gudanar Da Zanga-Zangar Rashin Bayyana Sakamakon Zaben Tambuwal

Published

on

Daruruwan mata sun gudanar da zanga-zangar lumana a Hukumar Zabe ta Jihar Sakkwato suna bukatar a bayyana Tambuwal a matsayin wanda ya samu nasarar lashe zaben Gwamna tare da cewar bayyana sakamakon zaben da aka yi a matsayin wanda bai kammala ba rashin adalci ne kuma lamari ne da ba za a yadda da shi ba.
Matan a karkashin jagorancin Kwamishinoni uku a Jihar, Farfesa Aisha Madawaki, Dakta Kulu Haruna da Hajiya Kulu Sifawa sun yi kira ga Hukumar Zabe da ta bayyana Tambuwal na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya samu nasara ba tare da bata lokaci ba.
Sifawa wadda ita ce Kwamishinar Lamurran Mata ta bayyana cewar al’umma sun zabi Tambuwal da mafi rinjayen kuri’u ya kuma tafiyar da mulki nagari tare da bunkasa rayuwar mata sama da kowace Gwamnati a tarihin jihar.
Ta ce sun gudanar da zanga-zangar lumanar ne domin nunawa duniya matsayin mata a jihar Sakkwato tare da kira ga Hukumar Zabe da ta bayyana wanda jama’a suka zaba a matsayin Gwamna domin samun zaman lafiya a jihar.
Kwamishinar Kimiya da Fasaha Dakta Kulu Haruna ta bayyana cewar mata a Kananan Hukumomi 23 sun zabi gudanar da zanga-zangar ne domin yaki da rashin adalcin da aka nuna na rashin bayyana Gwamna Aminu Waziri Tambuwal dan takarar jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya samu nasara da rinjayen kuri’u. “Abin da kawai muke bukata shine a yi mana adalci, wato a bayyana Tambuwal a matsayin zababben Gwamna domin samun zaman lafiya.” Ta bayyana.
Ita kuwa shugabar mata ta jam’iyyar PDP Hajiya Rabi Giyawa sukar Hukumar Zabe ta yi kan matakin da ta dauka a Sakkwato a zaben makon jiya ta na cewar a fili an sabawa dokokin Hukumar Zabe na bayyana zaben a matsayin wanda bai kammala ba don haka ta ce ya zama wajibi Hukumar Zabe ta bayyana Tambuwal a matsayin wanda ya zamo zakara a zaben.
Daga cikin matan da suka yi tattaki a zanga-zangar tun daga ofishin yekuwar neman zaben Tambuwal zuwa Hukumar Zabe akwai matar tsohon Gwamnan Sakkwato Hajiya Jamila Bafarawa da manba ta din-din-din a Hukumar Bayar da Ilimi Bai Daya (SUBEB) Hajiya Fatima Illo da sauran su.
Idan za a tuna dai a zaben da aka gudanar, Gwamna Tambuwal ya samu kuri’a 489, 558 a yayin da wanda ke bi masa baya Ahmad Aliyu na Jam’iyyar APC ya samu kuri’a 486, 145 wanda a kan hakan ne jami’ar tattarawa da bayyana sakamakon zaben Farfesa Fatima Mukhtar ta bayyana zaben a matsayin wanda bai kammala ba. A yanzu haka dai Hukumar Zabe ta Kasa ta bayyana ranar 23 ga wannan watan a matsayin ranar da za a gudanar da zaben a zagaye na biyu.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!