Connect with us

LABARAI

’Yan Sanda Sun Kama Mutum Daya Kan Kisan Dan Majalisa

Published

on

A ranar Talata ne, Rundunar ‘yan sanda ta Jihar Oyo ta ce, ta kama wani da ake zargi, wanda zai taimakawa ‘yan sandan wajen gano makisan dan majalisa a Jihar da aka kashe, Temitope Olatoye (Sugar).
A ranar Lahadi ne, rundunar ta sha alwashin kamo duk masu hannu a kan kisan na Olatoye.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar, Olugbenga Fadeyi, ya shaidawa wakilinmu a ranar Talata, cewa wata tawagar masu bincike ta ‘yan sanda a karkashin jagorancin mataimakin Kwamishinan ‘yan sanda, wanda ke jagorantar sashen binciken masu aikata laifuka da samar da bayanan sirri, sun kama wani da ake zargi (ba a bayyana sunan sa ba), a kan kisan dan majalisar na tarraya da aka yi.
Ya kara da cewa, ‘yan sandan suna gab da kama duk wadanda suke da hannu a kan kisan na Olatoye, ya ce wanda aka kaman yana bayar da bayanai masu mahimmanci ga ‘yan sanda.
“Mun kama mutum guda dangane da kisan dan majalisan yana kuma taimakawa ‘yan sanda da bayanai masu mahimmanci da za su kai ga kama duk masu hannu a kan aikata wannan mummunan aikin. Ina tabbatar maku, muna gab da kama makasan,” in ji shi.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!