Connect with us

FILIN FATAWA

Budurwata Ba Ta Haila, Hakan Falala Ce Ko Matsala?

Published

on

Tambaya
Assalamu alaikum dan Allah malam a taimaka min, matar da zan aura a yanzu haka auren bai fi wata biyu ba, shekararta 20 amma ba ta taba jinin haila ba. To malam wannan matsala ce ko kuma falalace? Sannan kuma za ta iya haihuwa? Malam A Taimakamin Don Allah (SWT).
Amsa
Wa’alaykumussala, to dan’uwa tabbas haila tana daga cikin alamomin da suke nuna cewa mace za ta iya daukar ciki, kamar yadda wasu malaman tafsirin suka fada, wannan ya sa lokacin da za’a yiwa matar Annabi Ibrahim bushara da haihuwa, sai da ta yi haila, saboda kasancewarta tsohuwa, haila kuma alama ce ta haihuwa, don haka duk matar da ba ta yin haila da wuya ta haihu.
Akan iya samun wasu matan ‘yan kadan wadanda suke iya haihuwa ko da ba su taba yin haila ba, saboda Allah mai iko ne akan komai.
Abin da nake ba ka shawara shi ne ku je wajan likitoci, don su gwada ta, in har suka tabbatar ba za ta iya haihuwa ba, kana iya hakura da auranta, saboda haihuwa ginshiki ne, daga cikin ginshikan da suke sa ayi aure.
Rashin yin haila ba falala ba ce, saboda hadisi ya tabbatar da cewa: “Haila jini ne da Allah ya hukuntawa dukkan ‘ya’yan Nana Hauwa’u” kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi mai lamba: 290.
Allah ne mafi sani
Zan Saki Matata Saboda Tana Da Cutar Aids?
Tambaya
Assalamu alaikum. Malam matata ta yi rashin lafiya, da aka gwada ta, sai aka ce tana da cutar aids, ni kuma an gwada ni amma an ce bani da ita, Sannan an gwada ragowar matana, suma an samu ba su da ita, gaskiya malam ina so zan sake ta, saboda kar ta shafe mu, amma ina neman shawara ?
Amsa
Wa’alaikum assalamu To dan’uwa cutar aids tana daga cikin cututtuka sababbi, wadanda ba’a tattauna su ba a manyan kundayen musulunci, saidai idan muka duba manufar da ta sa aka shar’anta saki wato tunkude cuta da matsala, daga daya daga cikin ma’aurata ko su duka, za muga ta tabbata a wannan cuta, tun da ilimin likitanci ya tabbatar da cewa cuta ce mai hadari kuma ana daukarta, don haka ya halatta ka sake ta, saboda wannan dalilin tun da malaman Fikhu sun halatta raba aure saboda cutar kuturta, kamar yadda hakan ya zo a Minahul Jalil Sharhu Muktasarul Khalil: 6\478 Cutar Sida kuma tafi kuturta tsanani.
Sannan ba za’a kalli cutuwar da za ta yi ba, bayan an saketa, domin yana daga cikin ka’idojin Sharia: kau da kai daga tunkude cutar da za ta shafi wani saboda cutar da za ta game, Cigaba da zama da ita zai jawo ka dauki cutar, kuma iyalanka su dauka, wannan yasa ba za’a waiga zuwa damuwarta ba a nan wurin.
Allah ne mafi sani.
Maziyyi Yana Karya Alwala?
Tambaya:
Assalamu alaikum wa rah matullah malam ina yi maka fatan alkhairi mal. Tambayata anan itace mutum ne yayi alwala yayi komai sai da yaje masallaci ya tayar da sallah sai maziyyi ya fito masa shin malam mutum za sallame sallar ne ko zai karasa ta kuma yaya hukuncin sallar tasa idan ya karasa allah ya karawa malam lafiya da wadatar zuciya na gode
Amsa:
Wa’alaikum assalam, ya wajaba ka yanke sallah, ka saké Alwala, an rawaito daga Aliyu (R.A) yace: “Na kasance mutum mai yawan maziyyi sai na umarci Mikdad ya tambayar min Annabi ﷺ sai ya ce maşa: Idan ya fito ka sake alwala, ka wanke azzakarinka, kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 266”
Allah ne mafi sani.
Na Yi Wankan Janaba, Sai Maniyyi Ya Sake Zubo Mini?
Tambaya
Assalamu Alaikum tambayata itace idan mata ta sadu da mijinta tayi wanka immidietly bayan ta gama tana zaune sai taji sperm ya zubo mata shin zata kara yin wani wanka ko kuma wanda tayi ya isa ?
Amsa
Wa’alaikum assalam, To idan sabuwar Sha’awa ce ta zo mata, ta zubar da maniyyi, ya wajaba ta sake wanka, amma idan saboda saduwar da suka yi ne a baya: za ta wanke wurin ne, ta sake alwala, amma babu bukatar sake wanka, wanda ta yi na farko ya isa. Duba Bidayatu Almujtahid 1\48 da Insaf 1\232.
Allah ne mafi sani.
Hukuncin Canja Abinci Da Mata Ke Yi A Gidajen Aurensu
Tamabaya
Assalamu alaikum Malam menene matsayin canjen abinci da mata keyi kamar mijinta ya ajiye mata semonbita ita kuma tafison masara sai ta canza.
Amsa
Wa’alakum assalam, ya kamata ya zama da iznin miji saboda hakan zai iya kawo rikici a tsakaninsu, tun da zai iya fahimtar rainuwa da rashin wadatar zuci.
Rayuwar aure tana tsayuwa akan girmama miji da nuna ba ki da sama da shi, da kimanta shi, Annabi ﷺ yana cewa inda zan umarci wani ya yiwa wani sujjada da na umarci mace ta yiwa MUJINTA sujjada.
Wannan yake nuna girman da muhimmanncin rashin Saba masa.
Allah ne mafi sani.
Watanni Nawa Miji Zai Iya Kaurace Wa Matarsa Ta Sunna?
Tambaya:
Tambaya ita ce؛ shin Tsawon wani lokaci ne ya halatta miji ya kaurace wa matar shi ta sunna kuma wani, Mataki ya dace ta dauka in har ya wuce period din da sharia ta halatta?.
Amsa:
Wa’alaykumussalam, Ya halatta ya kaurace mata tsawon watanni hudu kamar yadda Allah ya fadi a suratul Bakara aya ta: 226.
Bai halatta ya wuce hakan ba, in ya koma da kansa ya cigaba da saduwa da ita to Allah mai gafara ne game da abin da ya wuce, in har ba zai koma ba bayan watanni hudu sai ya sake ta kamar yadda aya ta 227 a cikin surar ta nuna hakan.
In ya ki komawa ya sadu da ita kuma ya ki saki sai taje wurin Alkali don ya bashi zabi tunda wata hudu ya cika ko ya dawo mata ko kuma ya sake.
Allah ne mafi Sani.
Yaushe Ake Yiwa Yaro Kaciya A Mahanga Ta Shari’a?
Tambaya
Assalamu Alaikum malam, ina tambaya ne a kan yiwa yaro kaciya shekara nawa ya kamata a yi masa?
Amsa
Wa alaikumus salam, To malam babu wani hadisi ingantacce wanda ya kayyade wani lokaci da za’a yiwa yaro kaciya, saidai malamai suna cewa:
Babbar manufar yin kaciya ita ce katanguwa daga najasar da zata iya makalewa a al’aura.
Wannan yasa ya wajaba a yiwa yaro kaciya dab da balagarsa, saboda idan ya balaga shari’a za ta hau kan shi kuma tsarkinsa ba zai cika ba, in ba’a yi masa kaciyar ba.
Daga cikin ka’aidojin malamai shine duk abin da wajibi ba zai cika ba sai da shi, to shi ma ya zama wajibi, amma mustahabbi ne ayi masa, tun yana dankarami, saidai wasu malaman sun karhanta yin kaciya ranar 7/ga haihuwa, saboda akwai kamanceceniya da yahudawa.
Don neman karin bayani duba Fathul-bary 10/349.
Allah ne mafi sani.
Hukuncin Matar Da Ta Yi Aure A Cikin Aure
Tambaya:
Assalamu Alaikum. Dr, shin mene ne hukuncin matar da ta yi sabon aure, ba tare da mijinta ya sake ta ba?.
Amsa:
Bayan bincike da tambayar malamai, na isa izuwa ga hukunci kamar haka:
1. Abin da ta yi mummuna ne a shari’ar musulunci saboda ta yi aure cikin aure.
2. Zaman da su ka yi da mijinta na biyu, a matsayin mazinaciya take, saboda haka duk kwanciyar da suka yi da wannan mijin na ta zina ne.
3. Yaran da su ka Haifa da mijnta na biyu, ‘ya’yansa ne, tun da bai san abin da ya faru ba a baya.
4. Har yanzu igiyar aurenta ba ta warware ba tsakaninta da mijinta na farko, saboda haka har yanzu ita matarsa ce saidai idan ya sake ta.
5. Mijinta na farko, zai iya dawowa da ita, ba tare da sake daura aure ba, saidai dole sai bayan ta tuba, domin ita a matsayin mazinaciyya take, kuma Allah ya hana auren mazinaciya.
6. Ya wajaba a gare ta ta yawaita istigfari saboda girman zunubun da ta aikata.
7. Zai yi kyau su je wajan Alkali wanda ya san shari’a, domin ya yi musu hukunci.
Allah ya kiyaye mu daga irin wannan aika-aikar.
Ana Gina Hukunci Ne A Kan Yakini Ko Mafi Rinjayen Zato
Tambaya
Assalamu alaikum,da fatan an wayi safiya lafiya. Don Allah Malam ka amma samin tambaya ta, ni ce malam ina fama da ciwon ulcer, duk lokaci ina jin hanjina yana yawan kuka, abin na samuna ko ina cikin sallah, idan abin ya yawaita sai in ga kamar alwalana ta karye, don Allah malam ka yi min bayani abin na damu na.
Amsa
Wa’alaikum assalam, in har ba ki fita daga hayyacinki ba kuma ba ki ji Kara ko iska ba daga mazaunanki, alwalarki tana nan. Ana Gina hukunci ne a musulunci akan yakini ko mafi rinjayen zato. Shakka ba ta kawar da tabbataccen hukunci kamar yadda hadisin Bukhari ya nuna.
Allah ne mafi sani.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!