Connect with us

KASASHEN WAJE

Akwai Alamomin Tambaya Kan Zaben Kano- Tarayyar Turai

Published

on

Masu sa ido na Kungiyar Tarayyar Turai wanda aka fi sani da EU a takaice sun bayyana cewa tashin hankali da sayen kuri’u da kuma firgita jama’a sun yi tasiri a yayin gudanar da zaben cike gurbin Gwamnan jihar Kano a arewacin Nijeriya.

Kungiyar ta EU ta ce ta damu matuka kan sakacin Hukumar Zabe Mai zaman Kanta wato INEC da hukumomin tsaro wajen magance tashin hankali da sauran matsalolin da aka samu a yayin gudanar da zaben na Kano.

A rahoton da ta fitar, EU ta ce, jami’anta sun shaida yadda wasu wakilai suka yi katsalandan da kuma sayen kuri’u a zaben na ranar 23 ga watan Maris.

Kungiyar ta ce, wasu ‘yan daba dauke da makamai su ne suka firgita jama’a tare da haifar da tarnaki wajen gudanar da zaben, lamarin da ya hana jami’anta da kuma ‘yan jaridu gudanar da ayyukansu cikin tsanaki.

Tuni Hukumar Zaben kasar, INEC ta bayyana Gwamna mai ci, Dakta Abdullahi Umar Ganduje na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya yi nasara a zaben domin ci gaba da jagorancin jihar a wa’adi na biyu.

A zaben da aka fara gudanarwa a ranar 9 ga watan Maris, dan takarar jam’iyyar PDP mai adawa, Injiniya Abba Kabir Yusuf ya bai wa Ganduje tazaar kuri’u dubu 26, amma INEC ta ce, Gandujen ya sha gaban Yusuf bayan kammala gudanar da cikon zaben a ranar 23 ga watan Maris.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: