Connect with us

LABARAI

Kotu Ta Kasa Sa Ranar Ci Gaba Da Sauraron Shari’ar Shaikh Zakzaky Da Matarsa

Published

on

Babbar Kotun Jihar Kaduna, wacce mai shari’a Gideon Kurada, yake shugabanta ta dage sauraron shari’ar da ake yi wa shugaban ‘Yan’uwa Musulmi, wadanda aka fi da kira da ‘Yan Shi’a, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, da Matarsa, Malama Zinat, har sai abin da hali ya yi.
Kamfanin dillancin labarai na kasa ya kawo rahoton da ke nuni da cewa, ana yi wa Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, shari’a ne a bisa tuhumar kisan kai, da yin taro ba bisa ka’ida ba, da makamantan hakan.
Mai shari’a Gideon Kurada, ya dage sauraron shari’ar ne har sai abin da hali ya yi a sakamakon nadin da aka yi masa na daya daga cikin Alkalan da za su saurari kararrakin zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya a Jihar Yobe.
Da yake magana da manema labarai jim kadan da dage sauraron shari’ar, Lauyan da ke jagorantar sauran Lauyoyin ‘yan’uwa Musumin, Femi Falana (SAN), cewa ya yi, baya ga kasantuwar Alkalin kotun baya nan, wanda yake karewar, (El-Zakzaky da Matarsa, Zinat), suna matukar bukatar neman magani, wanda hakan ne ma ya sanya ba su sami halartar zaman kotun ba.
Falana ya ce, sam ba a baiwa wadanda yake karewar kulawar da ya kamata a kan lafiyarsu ba tun daga ranar 14 ga watan Disamba, 2015, da ake tsare da su.
“Har yanzun ba a baiwa wadanda nake karewa kulawar da ta dace a kan lafiyarsu ba, duk da umurnin da kotu ta yi a kan hakan.
“An dage sauraron shari’ar, domin wadanda nake karewa suna da bukatar lokaci domin a duba lafiyarsu,” in ji Falana.
A baya, kamfanin dillancin labarai na kasa NAN, ya kawo rahoton cewa, kotun a ranar 22 ga watan Janairu, 2019, ta umurci gwamnatin Jihar Kaduna, da ta baiwa shugaban ‘yan’uwa Musulmin tare da Matarsa daman ganin Likitoci domin a duba afiyarsu.
Hakanan, a wannan ranar ne Alkalin kotun ya amince da janye tuhuma a kan wadanda ake tuhuma na uku da na hudu, Yakubu Yahaya da Sanusi Abdulkadir, wadanda ake tuhuma tare da shugaban na ‘yan’uwa Musulmin.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!