Connect with us

SIYASA

Nasarar Gwamna Ganduje Nasarar Al’ummar Kano Ce, inji Kashe Kobo

Published

on

An bayyana zaben da aka sake yiwa Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje da cewar zabi ne daga Allah, wannan jawabi ya fito daga bakin shugaban Jam’iyyar APC reshen Karamar Hukumar Gwale a Jihar Kano, kuma Babban Manajan Darakta gidan adana namun daji na Jihar Kano Alhaji Umar Yusif Kashe Kobo a lokacin da yake zantawa da Jaridar Leadershi Ayau a ofishinsa. Kashe Kobo ya ce, nasarar da Gwamna Ganduje ya samu al’amari ne daga Allah, musamman idan aka duba irin gagarumar Nasarar da ya cimma cikin shekaru hudu da suka gabata.
Alhaji Umaru Yusif Kashe Kobo ya ci gaba da cewa batun wannan nasarar abu ne daga Allah domin duk wanda ke Jihar Kano ya ga yadda Jam’iyyar APC ta yiwa Jam’iyyar PDP zigidir a zaben shugaban Kasa, majalisar Dattijai da kuma wakilan majalisar wakilai ta tarayya, ko kujera daya bata samu ba, wanda idan zaka tuna ba afahari ba daman na fada maka a wata tattaunawa da muka yi cewar sai na tabbatar da kayar da dan Takarar Kujerar Gwamna a karkashin tutar Jam’iyyar PDP wanda dan Karamar Hukumar Gwale ne, kuma alhamdulillahi tun daga akwatu mai lamba 001,002,003,004 har zuwa 005 ba wanda Jam’iyyata bamu kayar da Abba Kabir Yusif ba a mazabars ta Chiranchi.
Da yake karin haske kan yukurin tafiya kotu da Jam’iyyar PDP ke yi a ahalin yanzu Kashe kobo cewa ya yi wannan itace dabara a garesu maimakon kalaman da shugabansu ke yi inda yake fadin kowa agent, kowa jami’in tsaro kowa mai daukar hoto. Amma dai nayi zaton kamar yadda na karbi kayen da akayi min na majalisar dokokin jihar Kano duk da nasan akwai arigizon kuri’a da kuma wurren da ba’ayi amfani da card reader ba, duk da haka na sa hannu tare da karbar wancan sakamakon zabe. Su kuma sai suka ci gaba da farfaganda cewar an gudanar da tashin hankali da saurar munanan magangan wanda hakan ko kadan ba dai dai bane, kotu macece da ciki ba’a san abinda zata haife ba, duk da dai yanzu ana scarninig inji Kashe Kobo.
Da yake tsokoci kan abubuwan da wannan Gwamnati zata mayar da hankali akai a wannan zango na biyu Kashe Kobo yace a hukumarsa ta gidan adana namun daji yanzu akwai abubuwa muhimmai da za’a ci gaba da aiwatarwa musamman tabbatar da tsaro da kuma kawar da matsalar badala da ake ganin wasu bata gari na shiga da mata cikin gidan da dare, wanda hakan tasa yau kwana uku kullum da magariba sai na zo kofar shiga gidan Zoo duk wacce naga zata shiga na mayar da ita ko da kuwa cewa tayi mijinta ne a ciki, sai dai ta jira shi ya fito. Haka kuma cikin kwanaki 100 dana yi a matsayin shugaban hukumar wannan gida na samar da sabbin Uniform ga ma’aikata, Karo sabbin namun daji, gina dakuna masu zuwa domin yiwa kasa hidima da kuma inganta tsarin tsaron gidan baki daya. Akarshe Kashe Kobo ya bukaci jama’ar Jihar Kano su kara baiwa Gwamna Ganduje iirin wannan hadin kai domin ci gaba da kwararowa Kanawa romon demakardiyya.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!