Connect with us

RAHOTANNI

Lamido Ya Tofa Albarkacin Bakinsa Kan Zargin Atiku Da Kasancewa Dan Kamaru

Published

on

Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, ya tofa albarkacin bakin sa kan zargin da a ke yi na cewa Atiku Abubakar dan kasar Kamaru. Ya fadi hakan ne inda yayi kira ga jam’iyyar APC da magoya bayansu a kan su daina fadin wannan magana, saboda Najeriya kasa ce mai tsari.

Lamido ya bayyana hakan yayin da ya ke amsa tambayoyi kan abinda APC su ka yi a matsayin wakilan jam’iyyar PDP dan takarar shugaban kasa a zaben da aka kammala, Alhaji Atiku Abubakar, badan Najeriya bane.

Ya bayyana cewa muhawarar game da yadda Atiku ke da nasaba da kasa, wanda ya fara ne, a matsayin wadansu mutane suka fullo da maganar cewa Atiku badan Nigeriya bane, ya zama dole mu tashi tsaye domin magance wannan batun idan ba haka ba to za a samu faraka wato raba kan Jama’a a Afrika baki daya. “

Lamido ya lura cewa akwai matsala da yawa a cikin hadin gwiwar kasar, ya gargadi cewa “idan muka kasance a kan wannan kabilanci, addini da kabila daban-daban bambancin al’ummominmu ba za a iya dakatar da shi ba”.

“Zuciyata ta karaya kuma yanzu na fara damuwa game da yadda wasu jama’a suke nuna Atiku Abubakar a matsayin ba dan kasa ba wannan abin kunya ne bayan kowa ya sani haifaffen kasar nan ne “

“Ya zama  dole ne mu tashi mu kira  mutane akan wannan abun da ake fada domin hakan zai iya haifar da matsala a kasar mu “

“Ya kara da cewa duba da yadda jam’iyyar APC ta kasa ta shigar da batun cewa Atiku ba dan Nigeriya bane, sannan kuma bai cancanci yayi takara ba a matsayin shugaban kasa, sabisa ba dan Nigeriya bane. “

“A cikin  takarda da APC ta gabatar bisa jagorancinsa, Lateef Fagbemi, ya fadi cewa bai kamata Atiku ya fito takarar zabe ba sabida ba dan Nigeriya bane dan Kamaru ne, wanda hakan kuma ba daidai bane”.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!