Connect with us

LABARAI

 ‘Yan Sanda Sun Tabbatar Da Labarin Kashe Mutum 2 Da Garkuwa Da 3 A Kaduna

Published

on

Jami’an tsaron ‘yan Sandan jihar Kaduna a jiya Asabar sun tabbatar da kashe mutum biyu da garkuwa da mutum uku a ‘recreational resort’ dake karamar hukumar Kajuru a jihar Kaduna. Jami’in hulda da jama’a na ‘yan Sandan, DSP Yakubu Sabo, shi ne ya tabbatar da aukuwar hakan a wata sanarwa da ya fitar a Kaduna.

Sabo ya tabbatar da cewa lamarin ya auku ne cikin daren Juma’a, inda wadansu da ake zargin masu garkuwa da jama’a ne dauke da muggan makamai suka yi nasarar shiga wurin, inda suka bindige wadansu da tafiya da wadansu. Sai dai ya tabbatar da cewa; DPO ya tura jami’an tsaro wurin domin kwashe wadanda abin ya shafa zuwa asibitin St. Gerald.

Ya kara da cewa; binciken da suka yi ya nuna cewa wadanda abin ya shafa masu yawon bude ido ne, inda guda sha biyu daga cikin su sun fito ne daga jihar Legas. Sai dai ya tabbatar da cewa; za su yi kokarinsu wajen kubutar da wadanda aka yi garkuwa da su da kuma kame wadanda ake zargin da aikata hakan.

Ya roki al’umma da cewa; Kwamishinan ‘yan Sandan jihar, Ahmad Abdur-Rahman, yana neman al’umma da su taimaka musu da duk wani bayani da zai taimaka musu a bincikensu.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!