Connect with us

LABARAI

Boko Haram Ta Kashe Sojoji Biyar A Magumeri Da Ke Borno

Published

on

Rundunar Sojin Nijeriya ta ce mayakan kungiyar Boko Haram sun kashe mata sojoji guda 5, lokacin da suka kai hari sansaninsu da ke Magumeri a Jihar Borno. Mai Magana da yawun sojin, Ezindu Idima ya bayyana cewar bayan kazamin harin da mayakan suka kai, anyi artabu sosai da maharan, wadanda suka afkawa sansanin sojin da yawa domin satar abinci, abin da ya baiwa sojin damar dakile harin.

Kakakin sojin ya ce dakarunsu sun yi nasarar jikkata maharan da dama, yayin da suma suka rasa sojojinsu guda 5. Rundunar sojin Nijeriya, ta fitar da wannan sanarwar ce, bayan da a jiya Lahadi, tsagin mayakan kungiyar ta Boko Haram da ke yi wa kungiyar IS biyayya, ya yi ikirarin hallaka dakarun kasar 10, a farmakin da suka kaiwa sansaninsu da ke garin Magumeri da ke jihar Borno.

Majiyar tsaro ta ce, mayakan haye akan babura da manyan motoci sun far ma sansanin sojin da ke Magumeri mai tazarar kilomita 50 daga birnin Maiduguri da yammacin Juma’ar da ta gabata.

Mayakan sun shafe tsawon sa’o’i 4 suna cin karensu babu babbaka a sansanin, inda suka kwashe makamai kafin daga bisani a yi nasarar fatattakar su, da taimakon barin wutar dakarun sojin saman Nijeriya da karin wasu sojin na kasa da aka tura zuwa garin
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!