Connect with us

KASUWANCI

Farashin Man Fetur, Dizil Da Kalanzir Ya Karu A Watan Afrilu – NBS

Published

on

Farashin man fetur, dizil da kuma Kalanzir sun karu sassa da dama a cikin kasar nan a watan da ya gabata. Bayanin hakan Hukumar Kididdiga ta Kasa NBS ta sanar da hakan a cikin sababbin rahotannin ta a kan kayan.

Rahoton yaci gaba da cewa, farashin man fetur samfarin PMS, ya karu da kashi 0.4 bisa dari daga wata zuwa wata akan naira 145.9 na kowacce lita daya a cikin watan Afirilun shekarar 2019 daga naira 145.3 a cikin watan Maris na shekarar 2019, amma ya ragu da kashi 3.6 bisa zari.

A cewar rahoton na Hukumar ta NBC, Jihohin da farashin na man fetur yafi tashi sune, Bayelsa, inda nata kai naira 148.64, Kogi naira 147.88 Yobe kuma naira 147.82.

Rahoton na NBC yaci gaba da cewa, jihohin da suke da karamin farashi na man fetur sune, Katsina, inda take da naira 143.50, Zamfara 144.43 sai kuma babban birinin tarayar Abuja nada naira N144.67.

Rahoton ya kara da cewa, Farashin man dizil samfarin AGO kuwa ya karu da kashi 0.66 bisa dari daga wata zuwa wata da kuma kashi 12.88 bisa dari zuwa nair 230.67 na ko wacce lita daya a cikin watan Afirilu daga naira 229.16 a cikin watan Maris.

A cewar rahotln na NBS, jihohin da farashin su na man dizil ta tashi sune, Borno, inda akada farashin naira 249.50, Osun naira 245.55 sai kuma Neja naira 241.90.

Jihohi kuma masu karamin farashi rahoton ya ci gaba da cewa sune, Ekiti, inda take da naira 204.40, Ribas naira 218.00, Filato naira 219.11.

Mafi yawancin guraren hada-hadar kasuwanci da gidaje sunfi dogara ne kachokam a kasar nan wajen yun amfani da man fetur da man dizil don zubawa a cikin janaretocin su, musamman ganin cewar har yanzu samun isashiyar wutar lantarki daga babban layin sadarwar na wutar ana karancin samar da wutar.

Ba kamar man fetur, dizil da kalanzir an sabunta farshin su an kuma kara zakuda farashin kan fanfunan su a gidajen sayar da mai yadda zasu tafi daidai da yadda farashin yake a kasuwar duniya na danyen mai.

A watan da ya gabata, farashin danyen mai ya a kasuwar duniya samfarin danyen mai na Brent, ya karu a cikin watanni shida, inda ya kai sama da dala 74.25 na ko wacce ganga daya bayan da Shugaban kasar Amurka Mista Donald Trump ya sanar da daukar matakin kawo karshen daga kafa ga wasu kasashe don su sayi danyen mai daga kasar Iran ba tare da fuskantar takunkumin Amurka ba.

Bugu da kari, rahoton na Hukumar NBS ya sanar da cewar, farashin lita na Kalanzir ya karu da kashi 4.06 bisa dari daga wata zuwa wata da kuma kashi 13.57 zuwa naira 316.26 a cikin watan Afirulu ya kai naira 303.94 a cikin watan Maris.

A cewar rahoton, jihohin da nasu farashin yafi yawa sune, Filato 361.90, Anambra nada naira 353.47 sai kuma Enugu naira 353.33, inda kuma wadanda suke da farashi kadan ya Gombe ya kai naira 269.04, sai Legas nata ya kai naira 272.02, sai kum Nasarawa ya kai naira 287.45.

Har ila yau, farashin galan din kalanzir ya karu da kashi 1.77 busa dari daga wata zuwa wata, unda ya kai kashi 24.20 bis dari zuwa naira 1,211.99 a cikin watan Afirilu daga naira 1,190.89 a cikin watan Maris.

A cewar rahoton na NBC, jihohin da nasu yafi yawa su ne Gombe, inda take da naira 1,361.54, Enugu nada naira 1,322.73 sai kuma Jigawa nada naira 1,321.43.

Jihohi masu kuma, mafi karanci inji rahoton sune, Bayelsa nada naira 1,031.67, Akwa Ibom nada naira 1,071.36 sai kuma Delta nada Naira 1,071.36.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!