Connect with us

KASUWANCI

MTN Ta Biya Tarar Biliyan N230 Kan Rijistar Ba Bisa ka’ida Ba

Published

on

Kamfanin sadarwa na MTN ya biya tarar kudi naira biliyan 235 daga cikin jimillar tarar biliyan 330 da hukumar sadarwa ta  kasa ta dora masa.

Mataimakin shugaban hukumar, Farfesa Umar Dambatta ne ya bayyana hakan yayin wata hira da manema labarai a Abuja ranar Litinin.

Dambatta ya  kara da cewa, biyo bayan matsalar da kamfanin na MTN ya samu, ya ba wa ‘yan Najeriya damar iya saka hannun jari a kamfanin yanzu, bayan saka kamfanin da hukumar NCC ta yi a cikin kasuwar hannun jari ta Najeriya.

“Mun yi nasara wurin ba wa ‘yan Najeriya damar iya saka hannun jari a babban kamfanin MTN bayan saka kamfanin cikin jerin kasuwar hannun jari ta Najeriya,” in ji shugaban na NCC

Ya ci gaba da cewa, “Daga cikin yarjejeniyar da muka cimma wa da kamfanin MTN na biyan tarar kudi naira biliyan 330, to sun biya biliyan 235, saura ragowar yanzu,” in ji shi.

A watan Oktoban shekarar 2015 ne dai, hukumar sadarwa ta  kasa NCC, ta ci kamfanin tarar kudi naira tiriliyan 1.4 na yin rijistar layukan waya ba bisa  ka’ida ba.

To sai dai, bayan doguwar tattaunawa tsakanin kamfanin da gwamnatin tarayya, an rage tarar zuwa naira biliyan 330.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: