Connect with us

KASUWANCI

Ma’aikata Sun Bukaci Tsohon Minista Ya Maido Da Naira Biliayan 14.38 Da Ya Karkatar Daga Hukumar NEPZA

Published

on

Manyan Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya da ke a babban birnin tarayyar  Abuja sun bukaci da a gaggauta maido da naira biliyan 14.38  da aka cire daga cikin asusun hukumar NEPZA zuwa kamfanin NSEZCO.

Ma’aikatan sun bayyana hakan ne a lokacin da suka kira taron manema labarai a babban birin tarayyar Abuja a karkashin kungiyar ma’aikata ta ASCSN reshen Babban Birnin tarayyar Abuja.

Shugaban Kwamrade Isaac Ojemhenke sunyi zargin cewar, tsohon Ministan Ma’aikatar Masana’antu,Kasuwanci da zuba Jari Dakta Okechukwu Enelamah a bisa cire kudin daga hukumar ta NEPZA ta haramtacciyar wanda hukumar tayi kasafin su,

Acewar Kwamrade Isaac Ojemhenke yaso ya mayar da ayyukan hukumar NEPZA zuwa ga kamfanin NSEZCO.

Ya kara da cewa, Dakta Enelemah yana kokarin yaga an sayarwa da kansa shiyar kasuwanci ta jihar  Kano data Calabar,inda hakan ya sanya yi arigizo a cikin kasafin kudi na shekara 2019.

Sai dai a cikin sanarwar da Dakta Okechukwu ya fitar ya karyata zargin ma’aikatan, inda yace an kirkiro da hukumar ce don yi aiki na musaman a fannin tattalin arzikin kasa a shiyoyin.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!