Connect with us

LABARAI

APC Ta Kori Tsohon Gwamna Yari Daga Jam’iyya

Published

on

A yau ne jam’iyyar APC ta kori tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Abdul’aziz Yari daga jam’iyyar.

Jam’iyyar ta kori Tsohon GWamna Yari ne tare da mataimakin Shugaban Jam’iyya (yankin Arewa), Lawali Shuaibu wanda APC din ta ce, ya hada baki da Yari wurin yi wa jam’iyyar Angulu da kan zabuwa a zaben da ya gabata.

Wannan matakin na korar Yari daga APC ya biyo bayan zaman gaggawa da jam’iyyar ta APC ta gudanar a Gusau babban birnin Jihar Zamfara.

Sanarwar koran n a kumshe ne a cikin wata takarda da Shugaban jam’iyyar na jihar Zamfara, Alhaji Surajo Garba Mai Katako ya rattabawa hannu, Inda a ciki ya bayyana cewa, sun dauki wannan matakin ne biyo bayan samun tsohon gwamna Yari tsumu-tsumu da haifar da cikas ga jam’iyyar wanda ya kai ga rasa kujerar gwamna da sauran kujeru a zaben da ya gabata.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: