Connect with us

BIDIYO

Sharhin Fim Din ‘Sahabi’

Published

on

Suna: Sahabi.

Tsara labari: Nafisa Abdullahi.

Kamfani: iPRINCE MEDIA da MD Film Production.

Daukar Nauyi:  Abubakar Muhammad.

Shiryawa: Yunusa Mu’azu.

Bada Umarni: Kamal S. Alkali.

Sharhi: Musa Ishak Muhammad.

Jarumai: Ali Nuhu, Nafisat Abdullahi, Ibrahim Shehu, Tijjani Faraga, Ladi Muhammad, Sa’eed Nagudu, Shamsu Dan Iya da sauransu.

Shi dai fim din “Sahabi” an gina shi ne a kan labarin wata budurwa mai Suna Rabi (Nafisat Abdullahi). Rabi yarinya ce mai hankali da kuma tarbiya, domin kuwa kowa na alfahari da ita a cikin karkararsu, saboda iliminta, tarbiya da kuma hankali. Sai dai amma ta samu kanta a cikin rudu sakamakon yaudarar da malaminsu kuma saurayinta wato Sahabi (Ibrahim Shehu) ya yi mata wanda har ya saka ta samu juna biyu a waje ba tare da ta yi aure ba.

A farkon fim din dai an hasko Babar Rabi wato Salamatu (Ladi Muhammad) tana tankade a tsakar gida, kawai sai ga Rabi ta fito daga daki da gudu ta je ta tsuguna tana amai. A nan take Babartata ta karaso kanta tana tambayar ta mai yake damunta. Sai ta ce, babu komai, karshe ta yi mata wasu tambayoyi wanda ta tabbatar cewa juna biyu ne Rabi take dauke da shi. A nan ne ta fara tambayarta cewa ya aka yi ta samu juna biyu? Ita kuma Rabi tana cewa ita fa ba ta da wani juna biyu. Sai babarta ta ce to shikenan idan babanki ya dawo kya fada masa shi. Sai Rabi ta tashi da gudu tana kuka sai ta gudu ta shige daki.

Bayan Baban Rabi wato Malam Hudu (Tijjani Faraga) ya dawo ne, shi ne babartata ta ke ba shi labarin abinda ya ke faruwa da Rabi. Ai kuwa nan take ransa ya yi mummunan baci, nan take ya je ya sami Rabi a cikin daki ya rufe ta da fada yana ce mata ya aka yi ta samu ciki?. Nan dai ya ce mata idan bata fada masa wa ne ne ya yi mata ba sai ya yanka ta. Duba da yadda ta ga ransa ya baci, a nan take ta fada masa cewa ai Sahabi ne ya yi mata. Jin furucin sunan Sahabi da ya yi ya saka shi cikin wani dogon tunani da kuma samun kansa cikin mamaki, saboda bai taba zatan Sahabi zai iya aikata hakan ba. Domin ita babartata ma ana ce mata Sahabi ne cewa ta yi karya ne, sharri kawai take so ta yi masa.

Shi dai Sahabi wani matashi ne mai nutsuwa da kamun kai, ga shi da ilimi domin ya taso ne a gidan ilimi wato gidan kawunsa Malam (Ali Nuhu). Nutsuwar Sahabi da kamun kansa ne ta saka kullum kawunsa wato Malam ya ke kara kaunarsa, kuma kullum ya ke kara samun kaunar jama’ar gari, domin kuwa kai-tsaye suna kallonsa ne a matsayin magajin malam. Wannan kyakkwan zato da kowa yake yi wa Sahabi, shi ne yasa su kansu iyayen Rabi sun kasa yadda da ita a kan cewa Sahabi ne ya yi lalata da ita har ta samu juna biyu. Duk da cewa abinda ta ke fada gaskiya ne amma sam su ka ki yarda, hasali ma su sun fi yarda da shi fiye da ita Rabin duk da cewa sun san irin tarbiyarta, kuma sun san bata musu karya. Da abundai yaki-ci-yaki-cinyewa ne, sai Malam Hudu ya ce to kawai su tashi dukansu su tafi gurun mallam.

A lokacin da aka karaso kofar gidan, shi kuma malam yana cikin yana ganawa da wata ‘yar uwarsa tana ba shi shawarar cewa ya kamata ya sake aure tunda matarsa ta riga ta mutu. Suna cikin maganar ne, sai kawai Malam ya jiyo sallama a waje yana fita sai ya ga Malam Hudu da iyalansa. Bayan ya shigo da su sun zauna ne, sai aka umarci Rabi ta fadi abinda yake faruwa. Shi ne ta yi wa Malam bayanin abinda ya faru, kuma ta kara nanatawa cewa Sahabi ne ya yi mata wannan abu. Shi ma Malam da aka ce masa Sahabi ne, nan take ya shiga wani yanayi na mamaki da kokonto. Ana cikin hakan sai ga Sahabi ya shigo, da a ka tambaye shi me ya sani game da maganr sai ya ce, shi wlh sharri za a yi masa, hasali ma shi bai ma san Rabi ba, balle har ace sun yi wata mu’amala da za su samu damar aikata hakan.

A haka dai rayuwa ta ci-gaba da yi wa Rabi kunci, domin kuwa kowa ya ki yarda da abinda ta fada. Kullum iyayenta kara matsa mata su ke a kan sai ta fadi gaskiya a kan wa ne ne ya yi mata, domin har yanzu ba su yarda da abinda take fada ba. Ana cikin hakan ne Malam Hudu ya kori Rabi daga gidansa duk da cewa Yayan Rabi wato Haladu (Shamsu Dan Iya) da babarta suna ta ba shi hakuri a kan kada ya kore ta, amma ya ce  lallai-lallai sai ta bar masa gida.

Bayan Rabi ta bar gidan ba ta zarce ko’ina ba sai gidan Malam wato gidan da Sahabi yake. Shi ne ta fadawa Malam abunda ya faru, sai ya ce ta zauna a nan ta jira shi, bari ya je ya samu Malam Hudun. Ya je ya ba shi hakuri amma sam ya ce shi ya hakura da ita duk inda za ta je ta je. Da Malam ya dawo gida shi ne yace mata ta zauna a wancan dakin har zuwa a ga abinda zai faru a gaba.

Asirin Sahabi ya tonu ne bayan da wani lokaci da daddare ya shiga dakin da Rabi ta ke, ya same ta yana bata hakurin cewa da Allah ta yi hakuri ta yafe masa abinda ya yi mata. Sai ta ce za ta yafe masa amma sai dai idan ya yadda zai aure ta. Shi ne yake fada mata shi fa ba aure ne a gabansa ba, shi babban burinsa shi ne ya tafi birni ya yi karatu. Ashe duk abinda su ke yi Malam yana tsaye a bakin kofar dakin yana jin duk abinda suke tattaunawa. Ai kuwa kawai sai ya bude kofar dakin nan ya shiga ya samu Sahabi ya yi tsuru-tsuru a cikin dakin. Nan dai ya fada masa cewa ya ba shi mamaki, kuma daga yau bazai kara yarda da shi ba, kuma ya tabbata ko yana so ko ba ya so sai ya auri Rabi bayan ta haihu.

A karshe ma Rabi sai ta yi bari, daga nan kuma a ka saka ranar bikinsu aka daura aurenta da sahabi. Kuma ta amince masa ya tafi birni ya je ya karo karatun domin cikar burin da ya dade yana dauke da shi. A haka dai aka ci-gaba da rayuwa, kuma aka yafewa juna.

ABUBUWAN YABAWA.

Sunan fim din ya dace da labarin.

Labarin mikakken labari ne.

Fim din ya samu nasarar rike mai kallo har karshen shi.

An nuna irin yadda kyawawan dabi’u su ke janyowa mutum samun shaida mai kyau.

Jaruman suma sun yi kokari wajen isar da sakon yadda ake bukatarsa.

KURAKURAI

Daukan fim din ya yi duhu sosai.

Hotuna basu fita yadda ya kamata ba a gurare da yawa.

A lokacin da Malam Hudu yace su zo su tafi gidan malam, matarsa Salamatu take fada masa Malam ai dare ya yi, a yi hakuri a bari sai gobe mana. Sai yace lallai yanzu za su je komin dare, kuma aka nuna sun tafi a lokacin, amma kuma sai aka hasko su a gidan malam da rana.

A lokacin da Rabi ta zo gidan Malam take fada masa an koreta, an ji yana cewa ki jira ni bari in je gurun na shi. Kuma aka hasko har ya je ya dawo wanda hakan yake nuna cewa da lokacin da ta ke fada masa, da zuwan sa gurun Malam Hudu, da dawowarsa gurun Rabin duka fitowa daya ce. Amma an nuno shi da kaya har kala uku mabanbanta a fitowar.

Ya kamata a ce an nuna wata alaka a baya tsakanin Rabi da Sahabi, hakan zai sa idan an ce wani abu ya faru a tsakaninsu to ba za a ji mamaki ba. Amma kwatakwata ba a  nunawa mai kallo cewa akwai wata alaka a tskaninsu kafun abinda ya faru, ya faru ba.

Ba a nuna wani abu na hukunci ga Sahabi a kan abinda ya aikata ba, wanda zai iya zama izina ga masu dabi’a irin tashi.

KARKAREWA.

Fim din “Sahabi” ya nuna irin tasirin yadda kyakkyawar dabi’a take da tasiri a gurun mutane, duba da yadda kowa yake kyautatawa Sahabi zaton alkhairi. Fim din ya samu nasarar isar da sako, amma akwai kurakurai masu yawa musamman a bangaren aikin fim din. Ya kamata masu bada umarni su ringa tsayawa tsayin-daka wajen ganin sun magance duk wasu matsaloli kafun a sako fim ya karaso ga masu kallo.   
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: