Connect with us

WASANNI

Magoya Bayan Real Madrid Sun Zazzagi Bale

Published

on

Dan wasan gaba na Real Madrid, Gareth Bale yasha zagi da cin mutunci a wajen magoya bayan kungiyar a jiya akan hanyarsa ta komawa filin daukar horo domin cigaba da shirye shiryen kakar wasa mai zuwa.

Duk da cewa dan wasan ya shafe shekaru shida a kungiyar, amma har yanzu magoya bayan kungiyar basu gama amincewa dashi ba kuma shima kociyan kungiyar, Zinadine Zidane, ya bayyana cewa dan wasa Bale baya cikin tsarin ‘yan wasan da zaiyi amfani dasu a kakar wasa mai zuwa.

Sai dai duk da haka Bale ya bayyana cewa bashi da burin barin kungiyar a halin da ake ciki saboda yana da ragowar kwantiragi na shekara uku kuma yana daya daga cikin ‘yan wasa masu daukar albashi mai yawa a kungiyar.

Kamar yadda wasu rahotanni suka bayyana daga kasar Sipaniya, magoya bayan kungiyar ne dai suka taro akan hanya suka zazzagi dan wasan dan asalin kasar Wales akan hanyarsa ta tafiya filin daukar horo.

Wani rahoton kuma ya bayyana cewa wasu daga cikin ‘yan wasan kungiyar da suke tafiya tare da dan wasan basuji dadin abinda magoya bayan kungiyar suka yiwa Bale ba saboda a lokacin da suke yiwa dan wasan ihu kuma suna yabon ragowar ‘yan wasan kungiyar.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: