Connect with us

SIYASA

Zaben Shugannin Kasuwar Zuba: Ya kamata Al’umma Su Zabi Wadanda Za Su Kawo Ci Gaba —Talba

Published

on

A daidai wannan lokacin da ake gab da gudanar da zaben shugabanin kasuwar kayan marmari da ke Zuba, karamar hukumar Gwagwalada a yankin birnin tarayya, daya daga cikin ‘yan takarar shugabancin kasuwar Ibrahim Talba, ya yi kira ga dukkan ‘yan kasuwar da su tabbatar cewa, sun zabi shugabanin da za su bayar da gudummowa wajen bunkasa kasuwar.

Talban ya ce, a halin yanzu kasuwar ta fada cikin wani mawuyacin halin da take bukatar shugabannin da za su ceto ta daga wannan hali da wasu kalilan din mutane suka jefa ta a ciki, saboda son ransu.

Kasancewarsa daya daga cikin shugabannin da ke jagorantar kasuwar a halin yanzu, wanda kuma shi da kansa ya nuna gazawar da aka samu a wannan shugabanci, ya ce, a matsayinsa na maji a tsarin shugabancin kasuwar, bai yi nadamar kasancewa a wannan matsayi nasa ba duk da gazawar da gwamnatin ta su ta yi, domin kuwa, a cewarsa, ya sauke dukkan nauyin da ya doru a kansa a wannan matsayin da yake da shi.

Ya ce, daga cikin abubuwan da suka kara masa karfin gwiwar fitowa takarar shugabncin kasuwar shi ne, ya samu damar da zai kawowa kasuwar ci gaba mai dorewa, musamman wajen ganin kasuwar ta samu ‘yancin cin gashin kanta.

Talban ya ce, a yanzu haka kasuwar na cikin mawuyacin hali, musamman na rashin samar da magudanan ruwa da rashin yi wa kasuwar ciko duk da dimbin kudin da ake samu a wannan kasuwa. Saboda haka y ace yana daga cikin burisa ya tabbatar tsaftace kasuwar yadda masu hulda za su samu walwalar shiga da fita.

Haka kuma Talban ya yi alkawarin tafiya kafada da kafada da dattawan wannan kasuwa domin neman shawarwarinsu kasancewarsu wadanda suka ga jiya kuma suke ganin yau.  Su kuwa matasa wadanda ya yaba da kwazonsu wajen neman na kansu y ace zai karo fito musu da hanyoyin da su amfana fiye da yadda suke a halin yanzu.

Sannan ya nuni da muhimmancin zaman lafiya musamman a daidai wannan lokaci da suke fuskantar siyasar shugabancin kasuwar, saboda sai ya ce kasancewa wannan kasuwace da ta yi fice wajen zaman lafiya da kwanciyar hankali, yakamata su ci gaba da tafiya a kan wannan kyakkyawan tsarin, domin ita ce hanyar samun ci gaba.

Da ya juya kan abokan takararsa kuwa, su ma ya yi kira da babbar murya da cewa, kamar yadda suka sani cewa, Allah shi ke  bayar da mulki ga wanda ya so, to duk wanda Allah ya ba, su tabbatar da cewa, sun ba shi cikakken goyon baya domin ta haka ne zai samu nasarar da ake bukata.

Ga masu zabe kuwa, Talban ya ce, su tabbatar cewa, ba su yi zaben tumun-dare ba, sun zabi shugabannin da za su kawo ci gabansu, ba shugabannin da za su fifita kansu ba. Su kuma guji karbar kudi domin su zabi dantakarar domin yin hakan kamar sayar da ‘yancin da mutum ke da shin za zaben wadanda suka cancanta. 
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: