Connect with us

LABARAI

Wani Mutum Ya Kashe Kaninsa A Kano

Published

on

‘Yan sandan jihar Kano sun kama wani mutum mai suna Tijjani Yahaya mai shekaru 57 bisa zargin sa da caka wa kaninsa mai suna Aminu mai shekaru 20 wuka wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar sa.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya bayyana cewa Aminu ya mutu ne a asibitin kwararru na Murtala Mohammed inda ake kokarin ceton rayuwar sa.
Ya ce lamarin ya faru ne da misalign karfe 9:00 ya dare ranar Juma’a bayan an samu rashin jituwa tsakanin su wanda har yanzu ba’a san akan me ba.
Ya ce da Tijjani da kaninsa suna zaune ne a Kofar Ruwa dake karamar hukumar Dala. Ya kara da cewa wanda ake zargin ya daba wa kaninsa wuta mai kaifi a kirji ranar Juma’a 19 ga watan Yuli da misalign karfe 9:00 na dare.
Mun samu rahoto a ofshin dake Dala cewa wani mutum mai suna Tijjani Yahaya ya daba wa kaninsa mai suna Aminu Muhammad wuka mai kaifi a kirjin sa, a makarantar islamiyyar at Annandini dake kofar Ruwa a karamar Hukumar Dala, Jihar Kano.
‘An yi gaggawar kai Amuni zuwa Asibitin Kwararru na Murtala Mohammad inda ya ce ga garin ku nan yayin da ake kokarin ceto rayuwar sa. Ya ce an kama wanda ake zargin kuma mun samu wukar a wajen sa.
A cewar kakakin rundunar ‘yan sanda, ya bayyana cewa a binciken da suka yi sun gano cewa an sanju rashin jitiuwa ne tsakanin su wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar Aminu.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!